Rahotanni daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum ya shaida cewa sau 50 yana tsallake rijiya da baya daga hare-haren da mayakan Boko Haram ke kai masa.
Gwamnan ya shaida hakan ne a lokacin wata tattaunawa da ?an jarida a fadar gwamnatin Abuja bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.
Jaridar Daily Trust ta rawaito gwamnan na cewa sama da ?an Borno dubu 100 aka kashe a rikicin Boko Haram na tsawon shekara 12.
Sannan ya kuma shaida cewa akwai maya?a 2,600 da suka mi?a wuya, cikinsu akwai yara da matan maya?an da wasu iyalan tubabun maya?a.
Ya ce cikin wadanda suka mi?a-wuya akwai mutanen da aka tilastawa ?aukan makami, wasu kuma yara ne da basu mallaki hankalinsu ba.
Gwamna Zulum ya ce gwamnatin Borno ba ta da niyyar bai wa tubabun maya?an sisin kobo da sunan samun bayanai kan sauran maya?a.
Gwamnan ya ce ya tattaunawa da Shugaba Buhari kan maya?an da suka tuba, kuma ya ce shi bai ga wani dalili na ?in karban maya?an da suka mi?a-wuya ba.
Ana yi ta ce-ce-ku-ce dai kan tubabun maya?an da su ka roki gaffara. Akwai masu ganin ya kamata a yafe musu, wasu kuma na cewa a gurfanar da su.
