Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sako Wasu Daliban Bethel Baptist Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Yan Bindigar da suka sace daliban Makarantar Bethel Baptist sun saki ?alibai 15 daga cikin wa?anda suka sace a sakandaren ta Jihar Kaduna.

Shugaban ?ungiyar Kiristoci ta CAN reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ya shaida wa BBC Hausa cewa an saki ?aliban ne da daren Asabar bayan an biya ku?in fansa.

Ya ce har yanzu akwai yara 65 a hannun ‘yan bindigar, yayin kusan 53 suka ku?uta. A ranar 25 ga Yuli aka saki 28 daga cikinsu.

‘Yan bindigar sun sace yaran ne maza da mata a ranar 5 ga watan Yuli bayan sun afka makarantar tasu da ke kan Titin Kaduna zuwa Kachia a ?aramar Hukumar Chikun.

Related posts

Leave a Comment