Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda Ta Kafa Sabon Kwamitin Bincikar Kyari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kafa wani sabon kwamiti na cikin gida wanda zai yi bincike mai zurfi a kan Takardun da FBI ta Amurka ta gabatar wadanda suka janyo dakatar da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari.

Ana zargin Abba Kyari, wanda shine tsohon shugaban IRT da amsar rashawa daga hannun wani rikakken dan damfarar yanar gizo, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.

An ruwaito yadda Kwamitin bincike na ‘yan sanda wanda sifeta janar na ‘yan sanda, Alkali Baba da mataimakinsa Joseph Egbunike suke shugabanta ya samar da kwamitin cikin gida.

Barista Tijjani Mohammed, shugaban bangaren hukunta ‘yan sanda ne ya kirkiri kwamitin yayin da Sakataren hukumar, Alhaji Abubakar Ismaila ne ya rantsar da kwamitin.

Related posts

Leave a Comment