Hukumar Jami’ar Jos ta dakatar da ayyukan karatu tare da rufe ta baki ?aya saboda kisan ?alibai da ke ?aruwa a kusa da makarantar” jim ka?an bayan sassauta dokar hana fita da aka saka.
A cewar wata sanarwa da Rajistira Monday Danjem ya sanya wa hannu, an umarci dukkan ?alibai da su koma gida ko kuma wani wuri mai kwanciyar hankali har sai hankula sun kwanta.
Kazalika, hukumar makarantar ta dakatar da jarrabawar da ta shirya farawa ta shekarar karatu ta 2019/2020.
Matakin jami’ar ya biyo bayan kisan wasu matafiya Musulmai 27 da ake zargin matasan ?abilar Irigwe da aikatawa ranar Asabar da ta gabata a kan hanyar Rukuba da ke ?aramar Hukumar Jos ta Arewa.
Lamarin ya jawo gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita a ?ananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa.Article share tools
