Gwamnatin tarayya ta baiwa ?an Najeriya shawarar su tashi tsaye dan kare kansu daga hare-haren ?an Bindiga dake kaiwa.
Ministan harkokin ?an sanda, Muhammad Dingyadi ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai.
Yana amsa tambaya ne kan umarnin da gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya baiwa jama’ar jiharsa kan su mallaki makamai dan kare kansu.
Dingyadi ya bayyana cewa kowa na da ra’ayinsa kuma watakila gwamnan ya ga cewa, hakan ne zai kawowa jiharsa maslaha.
Yace amma abinda suke cewa, shine kada mutum ya mallaki makami ta hanyar da bata dace ba. Yace amma irin ya?in sunkuru da ?an Binduga suke, dole ne sai jama’a sun taimakawa gwamnati.
Yace shiyasa ma aka kawo ?an sandan cikin al’umma.
