Matsalar Tsaro: Lokaci Ya Yi Na Sanya Dokar Ta Baci A Arewa – Matawalle

Mai girma gwamnan Jihar zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa lallai yanzu lokacin sa dokar ta Baci a fannin tsaro musamman a jihohin arewa.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne yayin ganawa da mataimakin insfecta janar na Yan sanda na kasa Ali Janga a fadar gwannatin jihar zamfara yayin ganawar su a yau laraba.

Matawalle yace kusan kowace jiha a arewa na fama da nata salon ayyukan ta’addanci Wanda Kullum hakan na janyo koma baya ga yankin mu. Ya Zama dole a Dau mataki tun yanzu kamin lamarin ya durkusar damu gabada.

KARIN HASKE

SA DOKAR TA BACI A JIHA BA ZAI BA GWAMNONI DA SAURAN ZABABBU KO JAMI’AN GWAMNATIN DAMAR JAGORANCIN JIHOHIN SU BA DOMIN SHUGABAN KASA NE ZAI ZABI WANI JAMI’AN TSARON KASAR NAN DA YA AMINCE DASHI YA BASHI JAN RAGAMAR JIHAR NA WANI LOKACI

Kuna ganin hakan zai kawo karshen shakakin tsaron da ya addabi yankin mu na AREWA ?

Related posts

Leave a Comment