Ina Nan Akan Bakana Na Kowa Ya Nemi Makami Don Kare Kai – Masari

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamna jihar Aminu Bello Masari ya yi watsi da kiran kungiyar arewa (CNG) na yayi murabus saboda yace mutane su kare kansu daga yan bindiga.

Masari yace ba shine gwamnan farko da ya fa?awa mutane su kare kansu daga ta’addancin yan bindiga ba, kuma ya fadi hakan ne saboda shine mataki na karshe.

Gwamnan ya kara da cewa kiran da ake masa ya yi murabus daga kujerarsa wata alama ce ta rashin fahimtar halin da kasar nan take ciki gaba ?aya.

Jihar Katsina na ?aya daga cikin Jihohin dake fama da hare-haren yan bindiga, inda suke sace mutane domin neman ku?in fansa da kuma kashe su ba gaira babu dalili.

Da yake jawabi a wata ziyara da ya kai Jibiya, Gwamna Masari ya bukaci mutanen jihar Katsina su tashi tsaye su kare kansu daga yan bindiga.

A wani jawabi da shugaban ?ungiyar CNG reshen yankin arewa maso yamma, Jamilu Charanci, ya fitar, yace kiran da gwamnan yayi na mutane su kare kansu ya nuna cewa ba shi ke da akalar juya jihar ba. Charanci ya kara da cewa saboda haka gwamnan ya gaza sauke nauyin da aka ?ora masa na samar da tsaro, don haka ya yi murabus.

Da yake martani a wani jawabi da kakakinsa, Abdul Labaran, ya fitar, Masari yace wata barazanar tsirarun mutane dake ikirarin kare hakkin dan adam ba zata sanya ya yi murabus ba.

“A lamarin tsaro, gwamna shine shugaban jami’an tsaro a jiharsa, amma a suna ne kawai saboda shugabannin hukumomin tsaro ba daga hannun gwamna suke karbar umarni ba, daga manyan su na Abuja ne.”

“Masari ba shine gwamna na farko da ya fara wannan maganar ba. Duk jihar da mutanenta ba su saka siyasa a lamarin tsaron su ba, zaka samu shugabannin su suna kara musu karfin guiwa.” “Duk wanda yake ganin Masari ya yi murabus kan baiwa jama’ar da yake jagoranta muhimmanci da kara musu karfin guiwar su kare kansu, to sam baima fahimci sakon ba da kuma kundin tsarin mulki.”

Related posts

Leave a Comment