Ya Kamata Tubabbun Boko Haram Su Fuskanci Shari’a – Ndume

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sanata Ali Ndume, sanata mai wakiltar Borno ta kudu, yace mayakan Boko Haram da suka mika wuya, “Wa?anda akwai sauran burbushin ta’addanci a zukatansu, kamata yayi a binciko su, a hukunta su.” Da yake jawabi a Abuja, jim ka?an bayan ganawa da shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, sanatan ya jaddada cewa bai kamata a saki jiki da tubabbun lokaci guda ba, domin yin hakan akwai hatsari. Sanatan yace ya kamata gwamnati ta bi dokar ?asa da kuma ta kasa-da-kasa wajen amsar tubabbun yan…

Read More

‘Yan Bindiga Sun Bindige Kanin Sowore

Rahotanni daga Jihar Edo na bayyana cewar wasu Yan bindiga sun bindige Olajide, wanda kani ne ga mai gidan jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, har lahira. Sowore ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook ranar Asabar. Dan jaridan ya bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kasheshi a hanyarsa daga jami’ar Igbinedion dake garin Okada, jihar Edo. A cewarsa: “Masu garkuwa da mutane makiyaya sun kashe kanina dake biye dani, Olajide Sowore, kusa da Okada a jihar Edo, yayinda yake dawowa daga jami’ar Igbinedion inda yake karatun…

Read More

Neja: Zaratan Mafarauta Sun Hallaka Gaggan ‘Yan Bindiga 47

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar wasu Zaratan Mafarautar Gargajiya sun yi nasarar kashe ‘Yan bindiga 47 da suka hana mutanen Shiroro dake Jihar Niger zaman lafiya na dogon lokaci. Rahotanni sun bayyana cewar mafarautar sun kaddamar da harin ne a Magami dake tsakanin kananan hukumomin Shiroro da Rafi inda suka hallaka ‘Yan bindigar a ranar larabar da ta gabata. Majiyarmu tace ‘Yan bindigar sun dade suna amfani da yankin dake kusa da gabar ruwa wajen fakewa suna kaiwa jama’a hare hare a yankunan jihar. An…

Read More

Gwamnati Ta Rufe Layukan Sadarwa A Jihar Zamfara

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ba da umarnin rufe layukan sadarwan daukacin kamfanonin waya a Jihar Zamfara. Umarnin rufe layukan sadarwan ya fara aiki ne ranar Juma’a a wani mataki na ba wa hukumomin tsaro damar gudanar da aikinsu a Jihar Zamfara, wadda matsalar ayyukan ’yan bindiga ta yi kamari. ’Yan banga da mafarauta sun kashe ’yan bindiga 47 a NejaTsohon dan bindiga ya koma gidan jiya a KatsinaSanarwar da NCC ta fitar ta ce, “Ci gaban matsalar tsaro a Jihar Zamfara ya sa dole a rufe layukan sadarwa…

Read More

Addu’a Ce Kawai Maganin ‘Yan Bindiga – Matawalle

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan Jihar Bello Matawalle ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara su tsananta addu’o’i domin Allah ya kawo ?arshen matsalar ?an bindiga a jihar. Matawalle ya yi wannan kiran ne yayin wani taron addu’a na musamman da kwamitin tuntu?a ta Ulamau ta shirya a jihar. Gwamnan wanda ya hallarci sallar Juma’a a babban masallacin Gusau ya ce ya zama dole al’umma su taimakawa gwamnati da jami’an tsaro wurin samar da tsaro a jihar, wadda harin ‘yan Bindiga ya mayar da…

Read More

Adamawa: An Cafke Mutumin Da Ya Kashe Wanda Ya Maye Gurbinshi A Ofis

An kama wani matashi mai suna Iliyasu Suleiman, bisa zargin kashe wani mutum da aka dauke shi aiki don ma ye gurbinsa bayan an kore shi daga kamfanin da ya yi aiki kan zargin sata a jihar Adamawa. Mutumin mai shekaru 40, wanda ake zargi daga gundumar Ngurore da ke jihar Adamawa, kamfanin sabis ne ya dauke shi aiki a matsayin mai gadi a shekarar 2020, kuma an kore shi daga aiki a watan Yulin 2021 bayan an zarge shi da satar kadarorin kamfanin. A cikin wata sanarwa da kakakin…

Read More

A Yi Afuwa Ga Bijirarrun Soji Kamar Yadda Aka Yi Wa Tubabbun Boko Haram – Falana

Babban lauyan Nigeria mai rajin kare hakkin bil adama, Femi Falana (SAN), ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa sojoji 70 da aka samu da laifin bore afuwa, kamar yadda ya yi wa tubabbun ‘yan Boko Haram. An samu sojojin da laifin yi wa shugabanninsu bore a Maiduguri, Jihar Borno a shekarar 2014 kuma daga bisani aka yanke musu hukunci mai tsanani. Da farko an yanke wa sojojin hukuncin kisa amma a 2015, bayan Falana ya rika bibiyar shar’arsu, an sauya hukuncin zuwa daurin shekaru 10 a gidan gyaran…

Read More

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Bazama Neman Daliban Da Aka Sace

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta baza jami’anta cikin daji domin ceto daliban makarantar gwamnati ta Kaya ta jeka ka dawo a yankin Maradun. Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan SP Mohammed Shehu ya fitar ya tabbatar da cewa dalibai 73 ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su daga makarantar. Ya ce ‘yan bindiga da dama ne suka abka makarantar suka saci daliban. Wannan na zuwa bayan gwamnati ta karbi daliban kwalejin noma da lafiyar dabbobi ta Bakura da aka kubutar bayan sun shafe kwanaki a hannun…

Read More

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Bazama Daji Neman Daliban Da Aka Sace

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta baza jami’anta cikin daji domin ceto daliban makarantar gwamnati ta Kaya ta jeka ka dawo a yankin Maradun. Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan SP Mohammed Shehu ya fitar ya tabbatar da cewa dalibai 73 ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su daga makarantar. Ya ce ‘yan bindiga da dama ne suka abka makarantar suka saci daliban. Wannan na zuwa bayan gwamnati ta karbi daliban kwalejin noma da lafiyar dabbobi ta Bakura da aka kubutar bayan sun shafe kwanaki a hannun…

Read More

Yanzu-Yanzu: ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Masu Yawa A Zamfara

Rahotanni dake shigo mana yanzu daga jihar Zamfara na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata makarantar maza da mata da ke karamar hukumar Maradun kuma sun sace dalibai da dama. Mazauna garin Kayan Maradun sun shaida wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da safiyar Laraba kuma sun sace daliban da ya zuwa yanzu ba a kai ga sanin adadinsu ba. Rahotanni sun ce dalibai fiye da 400 ne suke makarantar lokacin da aka kai harin suna masu karawa da cewa daliban suna rubuta…

Read More

Mun Tattauna Da ?ana ‘Yan Sa’o’i Kafin Mutuwarsa – Na’Allah

Sanata Bala Na’Allah ya bayyana yadda yayi tattaunawar karshe da Danshi awanni kafin a kashe shi. Babban Dan Sanatan Captain Abdulkareem Bala Na’Allah an same shi matacce, a Dakin sa dake Malali ta Jahar Kaduna a ranar Lahadi. Marigayin Mai Shekaru 36 yayi aure kwanaki kadan, sun bar gawar shi bayan an kashe shi, a yayinda Wanda suka aikata laifin suka gudu. Dayake jawabi a gidanshi dake kan Hanyar Unguwar Gwamna a Kaduna a ranar Talata, Sanatan Wanda yayi tafiya kashashen waje a lokacin da Lamarin ya faru, yace akwai…

Read More

Kaduna: El Rufa’i Ya Haramta Cin Kasuwannin Mako-Mako

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta dakatar da cin kasuwanni mako-mako a wasu kananan hukumomi biyar na Jihar. An kuma haramta wa gidajen mai sayar da mai a jarka tare da haramta sayar da man a gefen titi. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Jihar Zamfara ta dauki irin wannan mataki a fadin jihar baki daya. Samuel Aruwan kwamishinan tsaro da harkokin cikin na Jihar Kaduna ya shaida wa BBC cewa an dauki matakin ne a kananan hukumomin guda biyar saboda dalilai na tsaro. Kananan…

Read More

Zamfara: Gwamna Matawalle Ya Kafa Sabbin Dokokin Tsaro

A wani mataki na ci gaba da ya?i da matsalolin tsaro a Jihar Zamfara, Gwamnan Jihar, Dr. Mohammed Bello Matawalle, ya kafa wasu sabbin dokoki har guda bawkai wa?anda kuma aka bu?aci al’ummar Zamfara su kiyaye su don taimaka wa gwamnatin jihar wajen cimma ?udurinta na neman ganin bayan matsalolin tsaro a jihar. Cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ayuba N. Elkanah, ya fitar a ranar Lahadi ta zayyano wa?annan dokoki da suka ha?a da: Haramta cin kasuwannin mako-mako a fa?in jihar, haramta…

Read More

Ina Fatan Rasuwar ?ana Ta Kawo ?arshen Matsalar Tsaro A Najeriya – Na’Allah

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sanata Bala Ibn Na’Allah, wanda miyagu suka halaka babban dan shi Abdulkareem a gidan shi da ke Malali jihar Kaduna, ya ce rayuwar dan shi ba ta fi ta kowanne dan Najeriya ba, duka ?aya suke kwanan shi ya ?are. A wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, Na’Allah ya bayyana fatansa na cewa ta yiwu mutuwar dan sa ta taka babban rawa wurin shawo kan matsalar tsaron dake addabar Najeriya musamman yankin Arewacin kasar. Sanata Na’Allah wanda baya kasar Najeriya…

Read More

Kaduna: Yadda ‘Yan Bindiga Suka Hallaka Dan Gidan Sanata

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar an gano gawar babban dan Sanata Bala Na Allah, Kyaftin Abdulkarim Bala Na Allah, a dakin kwanansa da ke Malali yankin ?aramar Hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna yashe cikin jini. An ruwaito cewa matukin jirgin mai shekaru 36, wanda ya yi aure kwanan nan, an daure shi kuma kana aka shake shi har ya mutu yayin da maharan suka tsere da motarsa da kayayyakinsa. Mai ba da shawara na musamman ga Sanata Na Allah, Garba Mohammed, yayin tabbatar da mummunan abin…

Read More

Katsina: Shugaban ‘Yan Bindiga Ya Gindaya Sharadin Yin Sulhu Da Gwamnati

A daidai lokacin da Arewa ke ?ara dulmiya a hannun ‘yan bindiga, a Jihar Katsina wani gogarman masu garkuwa da mutane mai suna Usman Idris da aka fi sani da Ruga Kachallah, ya nemi a biya shi diyyar dukkan buhunan hatsin sa da jami’an ‘yan sanda su ka banka wa wuta, kafin a yi sulhu da shi. Sai dai kuma Rundunar ‘Yan Sandan Katsina ta yi watsi da kalaman na sa, inda ta bayyana cewa sau hu?u ana sulhu da Ruga Kachallah, amma sai ya tayar da tubar sa. Kachallah…

Read More

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Hari A Birnin Zazzau

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar akalla mutane bakwai ne wasu yan bindiga suka sace yayin da suka kai hari a unguwar Zango a Samarun Zaria da ke jihar Kaduna. Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun afkawa unguwar ne ta hanyoyin shiga daban-daban misalin karfe dayan daren Juma’a a yayin da mutane ke barci. Wani shaida ya ce: “Yan bindigan sun kai hari wasu gidaje a yankin a yayin da suke ta harbe-harben bindiga na tsawon mintuna 30. “Dan uwa na ya fara kira na a waya, yana cewa…

Read More

Kwamitin Dake Bincikar Abba Kyari Ya Mika Rahotonsa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an kammala bincike kan zargin da ake yiwa tsohon kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari. Shugaban kwamitin da Sifeto Janar na yan sanda ya nada don binciken, DIG Joseph Egbunike. ya gabatar da kundin sakamakon binciken ga IGP Mohammed Alkali a ranar Alhamis, 26 ga Agusta, 2021. Kakakin hukumar yan sanda, CP Frank Mba, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki da yammacin ranar Alhamis a shafin hukumar. A jawabin, DIG Egbunike ya godewa IGP bisa yarda da kwamitinsa da…

Read More

‘Yan Siyasa Ne Suka Jefa Najeriya Cikin Matsala – Sanata Okorocha

Sanata mai wakiltar maza?ar Imo ta yamma Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar imo, ya yi zargin cewa ‘yan siyasar kasar nan na da hannu dumu-dumu a cikin tabarbarewar lamura da rashin hadin kai a tsakanin al’umman kasar. Okorocha ya bayyana cewa rashin bawa ‘yan kasa masu kishinta damar mulkar kasar na daya daga cikin abubuwan da suka sanya ake samun karuwar masu son a raba kasar. A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, tsohon gwamnan ya kara da cewa idan har masu rike da madafun iko…

Read More

Matsalar Tsaro: Buhari Ya Tura Dakarun Soji 100 Zamfara

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan jihar Bello Matawalle ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan bayar da umarnin aika Dakarun kar ta kwana na musamman don yaki da ‘yan bindiga a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Alhamis lokacin da ya karbi baukuncin babban kwamandan runduna ta takwas da sojin Najeriya da ke Sokoto da kwamandan rundunar hadin gwiwa na yankin arewa maso yammacin kasar na rundunar Hadarin Kaji. Gwamnan y ace ya ji dadin aike wa da dakaru na musamman har…

Read More