Rundunan ‘yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran mutumin da ake zargi dilar tabar wiwi ne, wanda ke gudanar da harkokinsa acikin kananan hukumomin Ganye, Jada, da kuma karamar hukumar Mayo Belwa dake jahar Adamawa.
Kakakin rundunŕn yan sandan a jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar akarabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Wanda ake zargin mai suna Zingina maigari dan shekaru ashirin da shida da haihuwa Wanda ke zaune a anguwar barde a cikin karamar hukumar Ganye a jahar Adamawa.
Sanarwan ta kara da cewa rundunan yan sandan ta musamman domin yaki da masuyin garkuwa da mutane, fashi da makami dama sauran laifukane suka kama wanda ake zargin.
Kwamishinan ya sandan jahar ta Adamawa C P Aliuy Adamu ya tabbatarwa hwamnatin dama al ummar jahar Adamawa da cewa rundunan zatayi iya kokarinta domin ganin an magance matsalar shaye shaye dama duk wasu laifuka a fadin jahar baki daya.
Kwamiahinan ya kuma kirayi al umman dake fadin jahar da akoda yaushe sukasance masu taimakawa hukumomin tsaro da wasu bayanai da zai taimakawa wajen kama masu aikata laifi a tsakanin Jamma a.
