Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun yi garkuwa da gwamman mutane bayan wani hari da suka kai a ?auyen Rimi da ke ?aramar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara ranar Juma’a.
Kwamishinan Ya?a Labarai Ibrahim Dosara ya tabbatar da kai harin, yana mai cewa kusan mutum 60 ne ‘yan bindigar suka sace, amma ya ce ba a tabbatar da adadin ba tukunna.
“A safiyar yau [Juma’a] mun tashi da labarin cewa ‘yan fashi sun afka wa ?auyen Rimi sun sace mutum 60, duk da cewa ba a tabbatar ba,” kamar yadda ya fa?a wa gidan talabijin na TVC.
Ya ?ara da cewa “jami’an tsaro da na gwamnati na ?o?arin tabbatar da ainahin adadin mutanen da kuma wa?anda aka ji wa rauni”.
“[Garin] Bakura hanyar ?arayi ce wadda ta dangane da Dansadau zuwa Birnin Gwari [a Jihar Kaduna] da kuma wasu sassa na Jihar Neja,” a cewarsa.
A ranar Litinin da ta gabata wasu ‘yan fashin suka sace ?alibai da malami da kuma iyalan malamin daga kwalejin harkokin noma ta garin na Bakura.
