Rahotanni daga Hedkwatar tsaro ta ?asa na bayyana cewar Rundunar sojin Najeriya ta ?aryata wasu rahotannin da suka ce sojojin da ke bakin aikin tsaron Kwalejin Horon Sojoji ta NDA bacci suke lokacin da ?an bindiga suka kai hari wanda ya kai ga kashe sojoji biyu da sace soja ?aya.
Sanarwar da babban jami’in ya?a labarai na rundunar sojin ya fitar Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyerr ya ce labarin da wasu jaridu suka wallafa ba gaskiya ba ne inda ya ?alubalanci jaridun su bayar da shaidar da ke tabbatar da jami’an sojin suna bacci lokacin da ?an bindigar suka kawo hari.
Labarin da ake ya?awa na cewa bacci ya kwashi jami’an da ke kula da kamarori na tsaro lokacin da ?an bindigar suka abka kwalejin NDA karya ce mara tushe ballantana makama.
Ranar Talata ne ‘yan Bindigar suka shiga marantar ta NDA suka kashe sojoji biyu suka yi garkuwa da daya.Kuma tun a ranar rundunar sojan ta ce ta dukufa domin kwato sojan nata.
Wasu rahotannin kafafen yada labarai da ba a tabbatar ba na cewa an tsinci gawar sojan nan da ‘yan fashi daji suka sace a kwalejin ta koyon aikin soji da ke Kaduna.
Rundunar sojin ta ce babban hafsan sojin Najeriya da hukumomin NDA sun kaddamar da bincike domin gano yadda har aka samu matsalar da ta ba ?an bindiga damar shiga kwalejin.
