Harin Makarantar NDA: Dattawan Arewa Sun Yi Kiran A Kori Mungono

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kungiyar dattawan arewa ta koka a kan tabarbarewar rashin tsaro sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai barikin Afaka dake NDA.

An ruwaito cewa Shugaban kungiyar CNEPD, Zana Goni ya bayyana hakan ne a wata takarda da kungiyar ta fitar ranar Laraba inda yace duk matsayin mutum da kuma inda yake zama ba zai tsira daga ta’addanci ba kenan a kasar nan, tabbas abubuwa sun lalace.

Kungiyar ta bukaci a tsige Monguno Sakamakon haka ne ya bukaci a tube mai bayar da shawara a kan harkar tsaro na kasa, Manjo janar Babagana Monguno mai murabus, matsawar yaki sauka da kansa.

Dattawan sun ce ya kamata a kawo garanbawul a kan harkar tsaron Najeriya gaba daya, kuma ya kamata manyan shugabannin tsaron kasar nan su fuskanci tuhuma.

Ya nuna alhininsa a kan yadda shugaba Muhammadu Buhari ya kyale Monguno ya cigaba da aiki duk da ya canja shugabannin tsaro.

Related posts

Leave a Comment