Katsina: Shugaban ‘Yan Bindiga Ya Gindaya Sharadin Yin Sulhu Da Gwamnati

A daidai lokacin da Arewa ke ?ara dulmiya a hannun ‘yan bindiga, a Jihar Katsina wani gogarman masu garkuwa da mutane mai suna Usman Idris da aka fi sani da Ruga Kachallah, ya nemi a biya shi diyyar dukkan buhunan hatsin sa da jami’an ‘yan sanda su ka banka wa wuta, kafin a yi sulhu da shi.

Sai dai kuma Rundunar ‘Yan Sandan Katsina ta yi watsi da kalaman na sa, inda ta bayyana cewa sau hu?u ana sulhu da Ruga Kachallah, amma sai ya tayar da tubar sa.

Kachallah shi ne babban gogarman ‘yan bindigar da ka hana ?aramar Hukumar Safana zaman lafiya da kewayen ta a Jihar Katsina.

Mazauna yankunan sun shaida wa wannan jarida cewa akwai dandazon ‘yan bindigar da ke ?ar?ashin Ruga Kachallah, wa?anda sun fitini garuruwa da ?auyukan yankin da garkuwa da satar shanu da dukiyoyi masu tarin yawa, gaba-ga?i.

Sai dai kuma wannan jarida ta ji cewa Kachallah ya na sana’ar da ta sa ya ke da farin jini sosai a garuruwan da ke kewayen Safana.

Ya mallaki motocin haya sosai wa?anda ake yi masa jigila garuruwan yankin ana tara masa ku?a?e.

Wannan sana’a da Kachalla ke yi ta samar wa matasa da dama aikin yi a kewayen. Kuma su na hamdala sosai ga Kachallah.

Mutanen karkarar Rulumbusawa, Yartsaku, Ma?era, Gimi da Chirena da ke cikin ?aramar Hukumar Safana a Jihar Katsina, sai sun nemi iznin Kachallah kafin su fita zuwa gonakin su.

A Arewacin Runka, gari na biyu wajen girma a ?aramar Hukumar Safana, can ma manoma sun mi?a wuya ga ‘Daular Kachallah’, gogarman ‘yan bindiga.

Ba kamar sauran ‘yan bindigar da ke ?oye a cikin daji ba, shi Ruga Kachallah a cikin garin Gimi ya ke zaune da iyalin sa. Ya san kowa, kowa ya san shi.

Kwanan nan mazauna garin sun hana jami’an ‘yan sanda kama wani yaron sa, wani ?an ta-kife, mai suna Gulbi.

An ce Kachallah na bai wa Gulbi shanun da ya sato, shi kuma ya na sayar masa.

Lokacin da mazauna garin su ka hana ‘yan sanda kama Gulbi, sun shaida wa Kwamandan Eriyar Safana, Dutsin-Ma, ?anmusa, Kurfi da Batsari, Aminu Umar-Daye cewa, ba za su bari a kama Gulbi ba, saboda idan aka kama shi, Kachalla cewa zai yi da ha?in bakin jama’a aka kama Gulbi, kuma a kan su zai huce haushin sa.

Haka dai Umar Daye ya ha?ura ya janye ‘yan sandan.

Sai dai kuma a ranar 25 Ga Mayu, jami’an tsaro sun koma har gidan Kachalla, ba su same shi ba, amma sun banka wa gidan wuta, su ka ?one masa buhunan kayan abinci. Sannan kuma su tafi da matan sa biyu.

Sai dai kuma ‘yan garin sun yi taron-dangi sun kashe wutar.

Daga nan fa Kachalla ya fusata, ya ri?a kama mutane, har sai da aka sakar masa mata biyu sannan ya saki wani malamin firamare da ya dam?e. Kuma ya ?ara ?aimi sosai wajen kama mutane ya na yin garkuwa da su, ana biyan sa diyya.

Sulhun Da Bai Tsinana Komai Ba:

Cikin 2016 ne Riga Kachalla ya ha?a kai da wasu fitinannun ‘yan bindiga da su ka ha?a har da Abdullahi Karki, wani tubabben ?an bindiga a yanzu, su ka yi al?awarin ajiye makamai a wani ?warya-?waryan bikin kar?ar tubar su a ?ar?ashin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa. An yi bikin a ?auyen Illela, cikin ?aramar Hukumar Safana.

Sai dai kuma ba a da?e da yin sulhun ba, sai dakarun Kachalla su ka koma bakin aikin kama mutane, su na yin garkuwa da su, ana biyan Kachalla ku?a?en fansa.

Bayan jami’an tsaro sun matsa lamba, wani dakaren Kachalla mai suna Jummah Tambai, ya kwashe iyalin sa ya koma Jihar Nassarawa, daga can kuma aka ce ya koma wani wurin da ake ha?ar ma’adinai a cikin dajin Jihar Osun.

Haka shi ma mahaifin Kachalla da ke zaune a ?auyen Sullu?awa cikin ?aramar Hukumar Safana, ya yi hijira ya koma garin Banki cikin ?aramar Hukumar Anchau, saboda ya kasa hana ?an sa Kachalla ci gaba da fashi, hare-hare da garkuwa da mutane.

Related posts

Leave a Comment