Zamfara: Gwamna Matawalle Ya Kafa Sabbin Dokokin Tsaro

A wani mataki na ci gaba da ya?i da matsalolin tsaro a Jihar Zamfara, Gwamnan Jihar, Dr. Mohammed Bello Matawalle, ya kafa wasu sabbin dokoki har guda bawkai wa?anda kuma aka bu?aci al’ummar Zamfara su kiyaye su don taimaka wa gwamnatin jihar wajen cimma ?udurinta na neman ganin bayan matsalolin tsaro a jihar.

Cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ayuba N. Elkanah, ya fitar a ranar Lahadi ta zayyano wa?annan dokoki da suka ha?a da: Haramta cin kasuwannin mako-mako a fa?in jihar, haramta sayar da man fetur a jarkoki, haramta zirga-zirgar babura da keke Napep a cikin birnin Gusau daga ?arfe 8 na dare zuwa 6 na safe, sannan daga ?arfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a sauran yankunan ?ananan hukumomin jihar.

Sauran dokokin su ne: Haramta wa gidajen mai saida wa motocin kasuwa fetur na sama da N10,000, haramta jigilar itacen hura wuta a sassan jihar, dakatar da jigilar dabbobi zuwa wajen jihar, da kuma binciken ?wa-?waf ga masu shigo da dabbobi jihar daga waje, sai kuma haramta wa babura ?aukar mutum fiye da biyu a lokaci guda.

Da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan ya ce Gwamna Matawalle ya shata wa?annan dokin ne a Juma’ar da ta gabata bayan da ya tuntu?i hukumomin tsaron jihar da sauran masu fa?a a ji a jihar.

Da wannan ne Kwamishinan ya ce, “Ina amfani da wannan dama wajen sanar da al’ummar Zamfara cewa, rundunar ‘yan sanda da takwarorinta a jihar a shirye suke wajen tabbatar da cewa ‘yan jihar sun kiyaye wa?annan dokoki.

“Daga yau Litinin, za mu kafa runduna ta musamman wadda za ta ri?a zagayawa sassan jihar don tabbatar da ba a yi wa wa?annan dokoki karan tsaye ba.”

Kwamishinan ya ?ara da cewa, jami’an tsaron jihar ba su ?auki aikinsu da wasa ba, don haka ba za su rangwanta wa duk wanda aka kama da laifin ?in yin biyayya ga wa?annan sabbin dokokin ba.

Daga nan, ya bu?aci ‘yan jihar da kowa ya ba da tasa gudunmawa wajen ci gaba da ya?i da matsalolin tsaro da ake yi a jihar. Tare da bai wa ‘yan jihar shawarar su zamo masu bin doka da oda a kowane lokaci.

Related posts

Leave a Comment