Kaduna: El Rufa’i Ya Haramta Cin Kasuwannin Mako-Mako

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta dakatar da cin kasuwanni mako-mako a wasu kananan hukumomi biyar na Jihar.

An kuma haramta wa gidajen mai sayar da mai a jarka tare da haramta sayar da man a gefen titi.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Jihar Zamfara ta dauki irin wannan mataki a fadin jihar baki daya.

Samuel Aruwan kwamishinan tsaro da harkokin cikin na Jihar Kaduna ya shaida wa BBC cewa an dauki matakin ne a kananan hukumomin guda biyar saboda dalilai na tsaro.

Kananan hukumomin da matakin ya shafa sun hada Birnin Gwari da Igabi da Giwa da Kajuru da Chikun.

Related posts

Leave a Comment