Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan Jihar Bello Matawalle ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara su tsananta addu’o’i domin Allah ya kawo ?arshen matsalar ?an bindiga a jihar.
Matawalle ya yi wannan kiran ne yayin wani taron addu’a na musamman da kwamitin tuntu?a ta Ulamau ta shirya a jihar.
Gwamnan wanda ya hallarci sallar Juma’a a babban masallacin Gusau ya ce ya zama dole al’umma su taimakawa gwamnati da jami’an tsaro wurin samar da tsaro a jihar, wadda harin ‘yan Bindiga ya mayar da ita baya.
“Addu’a shine babban makamin da zai iya maganin kowanne bala’i. Ya zama dole mu tuba ga Allah.” Kamfanin Dillancin Labari, NAN, ya ruwaito cewa an yi addu’o’in na musamman a dukkan masallatai Juma’a a Jihar.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren yan bindiga a arewa maso yammacin Nigeria. A baya-bayan nan wasu yan bindigan sun afka wata makaranta a jihar Zamfara sun sace dalibai kamar yadda rundunar yan sandan jihar ta tabbatar.
