Babban lauyan Nigeria mai rajin kare hakkin bil adama, Femi Falana (SAN), ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa sojoji 70 da aka samu da laifin bore afuwa, kamar yadda ya yi wa tubabbun ‘yan Boko Haram.
An samu sojojin da laifin yi wa shugabanninsu bore a Maiduguri, Jihar Borno a shekarar 2014 kuma daga bisani aka yanke musu hukunci mai tsanani.
Da farko an yanke wa sojojin hukuncin kisa amma a 2015, bayan Falana ya rika bibiyar shar’arsu, an sauya hukuncin zuwa daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali.
A wata wasika mai dauke da kwanan wata na 25 ga watan Agustan 2021, da ya aike wa shugaban kasa, Falana ya ce sojojin kawai sun nemi a basu mukamai da suka dace ne domin yaki da yan ta’addan a arewa maso gabas.
Babban lauyan ya ce ba laifin sojojin bane cewa ba a samar musu da makamai da sauran abuwan da suke bukata ba. Ya ce idan har gwamnati za ta karbar afuwar tubabbun yan ta’adda, sojojin da kawai nema suka yi a wadatar da su kayan aiki suma sun cancanci a yi musu afuwa.
