Sanata mai wakiltar maza?ar Imo ta yamma Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar imo, ya yi zargin cewa ‘yan siyasar kasar nan na da hannu dumu-dumu a cikin tabarbarewar lamura da rashin hadin kai a tsakanin al’umman kasar.
Okorocha ya bayyana cewa rashin bawa ‘yan kasa masu kishinta damar mulkar kasar na daya daga cikin abubuwan da suka sanya ake samun karuwar masu son a raba kasar.
A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, tsohon gwamnan ya kara da cewa idan har masu rike da madafun iko suka amince da za su samar da hadin kai a tsakanin al’umma, shakka babu za a cimma manufa.
Sai dai kuma ya bayyana hakan a matsayin abu mai wahala saboda mafi akasarinsu kansu kadai suka sani, ba su damu da damuwar jama’ar su ba.
“Mu muka janyo matsalolin da ake ciki a kasar nan ba kowa ba, a yanzu ‘yan siyasa na yi ne domin cimma bukatun kansu, yawancin wadanda ke neman shugabanci dama suke nema su yi abun da suke nema a kan mulki.”
Har ila yau ya kuma zargi ‘yan siyasa da nuna bangaranci da kuma siyasar kabilanci, sannan ga lamarin rikicin addini da ake amfani da ita wajen kara raba kan al’umma.
Ya kuma ce hanya daya da za a iya bi don magance wannan matsala ita ce wayar da kan ‘yan kasa, ta yadda za su fahimci irin makircin da ake shiryawa da kuma manufar yin hakan. Ya kara da cewa:
”Matsalar ita ce ba su gane ba ne, idan aka ganar da su za su fahimci cewa irin wadannan matsaloli ne suka hana Najeriya ci gaba, su suka haifar da rashin aikin yi da talauci da kuma siyasar kisa da cutar da jama’a.”
Ya kuma yi nuni ga bukatar ganin an janyo matasa a jiki, ta yadda za a ba su dama su nuna bajintarsu a bangarorin shugabanci, ta yadda ba za su bayar da kunya ba duk lokacin da aka sakar musu ragama.
