Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Hari A Birnin Zazzau

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar akalla mutane bakwai ne wasu yan bindiga suka sace yayin da suka kai hari a unguwar Zango a Samarun Zaria da ke jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun afkawa unguwar ne ta hanyoyin shiga daban-daban misalin karfe dayan daren Juma’a a yayin da mutane ke barci.

Wani shaida ya ce: “Yan bindigan sun kai hari wasu gidaje a yankin a yayin da suke ta harbe-harben bindiga na tsawon mintuna 30. “Dan uwa na ya fara kira na a waya, yana cewa masu garkuwa da mutane sun shigo Zango, daga nan na fara jin karar harbin bindiga a gaban gidanmu.

Nan take na tafi na duba ‘ya’ya na na gano suna barci.” “Na leka ta tagar; domin ina tunanin sun riga sun shigo gidan mu ne. Sun buga kofar gidan mu sau uku sannan suka sha ruwa a famfon da ke kofar gidan a waje.

“Duk wanda ka kira sai ya ce maka sun wuce ta kofar gidansu. Kawo yanzu an fada masa mutum bakwai aka sace. Abin da muka sani kenan yanzu. Sun shiga gidaje da yawa. Ina da tabbacin sun sace fiye da hakan.”

Kakakin yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige bai daga wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana ba a lokacin hada wannan rahoton.

Related posts

Leave a Comment