Sanata Bala Na’Allah ya bayyana yadda yayi tattaunawar karshe da Danshi awanni kafin a kashe shi.
Babban Dan Sanatan Captain Abdulkareem Bala Na’Allah an same shi matacce, a Dakin sa dake Malali ta Jahar Kaduna a ranar Lahadi.
Marigayin Mai Shekaru 36 yayi aure kwanaki kadan, sun bar gawar shi bayan an kashe shi, a yayinda Wanda suka aikata laifin suka gudu.
Dayake jawabi a gidanshi dake kan Hanyar Unguwar Gwamna a Kaduna a ranar Talata, Sanatan Wanda yayi tafiya kashashen waje a lokacin da Lamarin ya faru, yace akwai bukatar a zama masu kula akan Matsalolin tsaro dake fuskantar Kasa.
Yace ya tattauna da Danshi akan Matsalar Tsaro awanni kafin a Kashe shi.
“Tun lokacin da Abdulkareem ya mutu, abubuwa da dama sun cigaba da faruwa Wanda suka rage man zafin jimamin mutuwar sa gareni. Nayi magana dashi da Misalin karfe 9:27 a ranar Asabar. Kuma na rantse da Alkur’ani Mai girma, abunda muka tattauna dashi shine tsaro. Abunda na sani shine saura awanni 8 ya mutu.
Na’Allah Wanda yayi jawabi akan tsaro, ya gargadi Yan siyasa dasu daina amfani da damar Lamarin domin radin kansu.
