Kwamitin Dake Bincikar Abba Kyari Ya Mika Rahotonsa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an kammala bincike kan zargin da ake yiwa tsohon kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari.

Shugaban kwamitin da Sifeto Janar na yan sanda ya nada don binciken, DIG Joseph Egbunike. ya gabatar da kundin sakamakon binciken ga IGP Mohammed Alkali a ranar Alhamis, 26 ga Agusta, 2021.

Kakakin hukumar yan sanda, CP Frank Mba, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki da yammacin ranar Alhamis a shafin hukumar.

A jawabin, DIG Egbunike ya godewa IGP bisa yarda da kwamitinsa da mambobinta da wannan aiki na bincike mai muhimmanci.

“Kwamitin ya fara bincike ba tare da bata lokaci ba kuma wannan kundin rahoton ya kunshi diddigi da gaskiyar abinda ya faru.

Hakazalika kundin ya kunshi maganganun Abba Kyari da wasu da ke da alaka da lamarin.”

Bayan gabatar da rahoton, IGP Alkali ya godewa kwamitin bisa aikin da sukayi kuma yayi alkawarin cewa za’a duba rahoton kuma za’a dauki matakin da ya kamata.

Related posts

Leave a Comment