Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar an gano gawar babban dan Sanata Bala Na Allah, Kyaftin Abdulkarim Bala Na Allah, a dakin kwanansa da ke Malali yankin ?aramar Hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna yashe cikin jini.
An ruwaito cewa matukin jirgin mai shekaru 36, wanda ya yi aure kwanan nan, an daure shi kuma kana aka shake shi har ya mutu yayin da maharan suka tsere da motarsa da kayayyakinsa.
Mai ba da shawara na musamman ga Sanata Na Allah, Garba Mohammed, yayin tabbatar da mummunan abin da ya faru, ya ce maharan sun samu shiga gidan ne ta rufin bayan gidansa.
Ya ce wani mai gadin makwabcinsa ya lura da cewa an bude kofar gidan marigayin tare da yin alama wanda ya kai ga gano gawar matukin.
An rawaito cewa Sanata Na Allah, wanda a halin yanzu baya Najeriya, yana da ‘ya’ya uku wadanda dukkansu matukan jirgi ne.
Da yake magana da ‘yan jarida Garba Mohammed ya ce aa yi sallar jana’izar marigayin a Yahaya Road yayin da aka a bunne shi a makabartar Unguwan Sarki.
