DAGA BASHIR ADAMU, JALINGO Rahotannin dake shigomana yanzu daga Jihar Taraba na cewa, Gwamna Dr. Agbu Kefas ya haramta hako ma’adinan Kasa a dukkanin fadin Jihar. Gwamnan ya fadi hakanne lokacin da yake ganawa da Sarakunan Gargajiyan Jihar, a Gidan Gwamnati dake Jalingo. Inda ya umurci Sarkunan a matsayin su na Iyayen Kasa, ya zama wajibi gwamnati ta hada kai dasu wajen kawo karshen matsalar tsaron da Jihar ke fama dashi. “Jihar Taraba kamar sauran Jihohi dake Kasannan, na fama da matsalolin rashin tsaro da ya kunshi, Yan Fashin Daji,…
Read MoreCategory: Tattalin Arziki
Tattalin Arziki
Kano: Zan Cigaba Da Bincikar Faifan Bidiyon Dalolin Ganduje – Muhuyi Rimin-Gado
Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci (PCACC) a jihar Kano, Muhuyi Rimingado ya sha alwashin ci gaba da binciken tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan batun zargin karbar cin hancin wasu daloli. Muhuyi ya ce binciken zai ta’allaka ne akan badakalar Daloli da aka ga gwamnan a wani faifan bidiyo na karba daga wurin ‘yan kwangila yana durawa a aljihunsa. Sabon Gwamna Abba Kabir a ranar Laraba 21 ga watan Yuni ya dawo da Muhuyi kujerarsa bayan dakatar da shi da tsohon Gwamna Ganduje ya yi…
Read MoreBan Taba Karbar Sammaci Daga EFCC Ba – Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta i?irarin mawa?in nan Femi Kuti da ya yi a kansa, wanda ya ce Hukumar EFCC ta gayyace shi kan zargin sha’anin ku?i bayan wa’adinsa ya ?are a matsayin mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa. A baya-bayan nan mawa?in ya ce tsohon shugaban kasar ya ta?a zuwa EFCC a matsayin wanda aka yi wa tambayoyi ko gudanar da bincike a kan shi, sai dai wata sanarwa da tsohon shugaban ya fitar ta musanta hakan.
Read MoreCire Tallafin Mai: Kamfanin NNPC Ya ?ara Farashin Man Fetur
Kamfanin man fetur na ?asa NNPC ya tabbatar da cewa ya ?ara ku?in litar mai a ?asar. A wata sanarwa da ta kamfanin ya wallafa a shafinsa na twitter, kamfanin ya ce ya yi ?arin farashin domin yin daidai da halin da ake ciki. Kuma ya ro?i afuwa kan wahalhalun da hakan zai iya haifarwa. Hakan dai na zuwa ne bayan shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar, a lokacin rantsar da shi cewa gwamnati ta dakatar da tallafin. Tun bayan furucin sabon shugaban ?asar ne aka fara ganin dogayen…
Read MoreNajeriya Ta Cimma Yarjejeniyar Dawo Da Kadarorinta Daga Saudiyya
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta cimma yarjejeniya da ?asar Saudiyya don ganin an kara samun nasarar kwato kadarorin gwamnati da aka sace. Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa, yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Jeddah da hukumar yaki da rashawa ta Saudiyya NAZAHA, ya ce hakan zai taimaka wajen dakile masu aikata rashawa. Abubuwa da shugaban na EFCC da tawagarsa suka tattauna a takwarorinsu na Saudiyya a ziyara da suka kai, ya hada da yadda za a kara kaimi wajen kwato kadarori da wasu ke sacewa su kai…
Read MoreBadakalar Kudi: EFCC Ta Damke Tsohon Ministan Lantarki Sale Mamman
Jami’an hukumar ya?i da cin hanci da hana yi wa tattalin arzi?in ?asa ta’annati sun kama tsohon ministan lantarki na Najeriya, Injiniya Saleh Mamman, wata majiya a ma’aikatar lantarki ta tarayya ta shaida wa BBC. Kafofin ya?a labaran ?asar sun ce EFCC ta kama Saleh Mamman ne tun da sanyin safiyar Laraba inda suke ci gaba da tsare da shi a shalkwatar hukumar da ke Abuja. Sun ce kamen na da ala?a da zargin almundahanar wasu ku?a?e kimanin naira biliyan 22. Zuwa yanzu, ba a ji wani martani daga ministan…
Read MoreBashin Dala Miliyan 800 Da Buhari Ya Karbo Daga Bankin Duniya Abin Takaici Ne – Cibiyar Sa-ido
Cibiyar sa-ido kan ayyukan majalisar dokokin Najeriya, CISLAC ta koka kan bashin dala miliyan 800 da gwamnatin kasar ta karbo daga Bankin Duniya, domin rage radadin cire tallafin man fetur. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce yin hakan wani bakon abu ne, saboda idan an daina bayar da tallafin tun a watan Afrilu, to kamata ya yi a mayar da kudaden da gwamnatin ta karbo daga babban bankin duniya. Shugaban kungiyar ta CISLAC, Awwal Musa Rafsanjani, ya shaida wa BBC cewa a ganinsu, idan aka kar?o bashi…
Read MoreIna Fatan Sabuwar Gwamnati Za Ta Dora Daga Inda Na Tsaya A Yaki Da Rashawa – Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce cin hanci da rashawa ya kasance babbar barazana da ?asashe ke ci gaba da fuskanta. Ya bayyana haka ne jiya a fadarsa da ke Abuja, yayin da ya kar?i bakuncin shugabannin gudanarwar Kotun ?a’ar Ma’aikata karkashin jagorancin shugabanta, Danladi Yakubu Umar. Buhari ya ce yana fatan irin kokarin da gwamnatinsa ta yi wajen yaki da cin hanci da rashawa, ita ma gwamnati mai zuwa za ta ?ora a kan haka. Ya bayyana Kotun ?a’ar Ma’aikata a matsayin muhimmiya ce wajen yaki da rashawa da gwamnatinsa…
Read MoreBabban Banki Ya Amince A Cigaba Da Amfani Da Tsoffin Kudi
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce a yanzu al’ummar kasar za su iya ci gaba da amfanin da tsofaffin takardun kudi na naira 200, da 500 da kuma 1,000. A wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Litinin da daddare, wadda ta samu sa hannun mukaddashin daraktan yada labarai na bankin, Isa AbdulMumin, bankin ya ce ya yi hakan ne domin jadadda bin doka irin ta gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Sanarwar ta ce, “Bisa yin biyayya ga halayyar girmama shari’a ta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, da kuma na ayyukan Babban…
Read MoreKarancin Kudi: An Bukaci Buhari Da Emefiele Su Yi Murabus
Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gamayyar ?ungiyoyin kare hakkin ?an adam a Najeriya sun yi kira cikin gaggawa ga Buhari da Gwamnan Babban Banki Godwin Emefiele su yi murabus daga mukamansu sakamakon gazawa wajen magance matsalar kudi. A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban gamayyar kungiyoyin Emmanuel Onwubiko yace kungiyoyin sun koka kan irin halin ko in kula da gwamnan babban banki Emefiele, da shugaba Buhari suka yi wa umurnin kotun kolin, inda ya ce sun gallaza wa ‘yan Najeriya azaba kan…
Read MoreBabban Banki Ya Amince A Cigaba Da Amfani Da Tsoffin Kudin ?500 Da ?1000
Sabbin rahotanni dake fitowa sun bayyana mana cewa, babban bankin Najariya, CBN ya amince a ci gaba da amfani da tsaffin kudaden Naira 500 da 1000. Jaridar the Cable ta ruwaito cewa, bankunan Zenith, UBA, da GTB a Legas sun bayar da tsaffin kudaden Naira a yau. Hakanan kuma wani jami’in daya daga cikin bankunan da jaridar ta zanta dashi ya bayyana cewa, sun samu umarnin yin hakan ne. ‘Yan Najeriya dai sun shiga cikin tashin hankali tsawon lokaci sakamakon karancin kudi da matakin da babban banki ya ?auka na…
Read MoreMun Cire Sama Da Mutum Miliyan 100 Daga Talauci – Ministar Jin Kai
Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta ce ta kashe naira biliyan 35.5 kan shirye-shiryen taimakawa al’umma a Jihar Taraba tun lokacin da ta ci mulki. Ministar Jin-?ai da kare Afkuwar Bala’i ta Najeriya Hajiya Sadiya Farouq ce ta bayyana haka a Jalingo babban birnin jihar, yayin da take wata tattaunawa da wa?anda suka ci moriyar shirye-shiryen. Ministar wadda shugabar shirin a jihar Beatrice Kitchina ta wakilta ta ce mutum sama da miliyan 100 sun fita daga cikin matsanancin talauci dalilin wannan shiri,…
Read MoreWa’adin Tsoffin Kudi: Ba Mu Saba Umarnin Kotu Ba – Ministan Shari’a
Antoni Janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami a ranar Alhamis ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai saba umurnin kotun koli ba kan batun wa’adin daina amfani da tsaffin kudi da wasu gwamnonin jihohi suka yi kararsa. Malami ya ce idan dai doka ake magana, akwai zabi daban-daban, ya yi wannan jawabin ne a wurin taron ministoci karo na 67 da aka yi a gidan gwamnati a ranar Alhamis. A ranar 8 ga watan Fabrairu ne kotun kolin ta bada umurni na hana babban bankin kasa, CBN, bada wa’adin…
Read MoreGwamnatin Bauchi Ta Karbi Dala Miliyan Biyu Daga Bankin Duniya – Bala Mohammed
Daga Adamu SHEHU Bauchi Gwamnatin Jihar Bauchi ta karbi zunzurutu kudi na dalar Amurka miliyan biyu daga asusun Bankin duniya da zimmar kawar da matsalar ambaliyar ruwa da kuma zaizayar kasa da ya addabi kana nan hukumomimin Jihar baki daya, Gwamnan Jihar Bala Abdulkadir Mohammed ne ya saida haka a lokacin wani zama na musamman da masu ruwa da tsaki na yankunan da wadan nan matsaloli sukafi ta gaiyyara wa a shekarun baya. Taron ya gudana ne a dakin taron da ke yankin rundunar sojin kasa dake Bauchi, tare da…
Read MoreKaduna: El Rufa’i Ya Umarci Ma’aikatun Gwamnati Da Karbar Tsoffin Kudi
Gwamnatin jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya umarci ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar da su tabbatar cewa hukumominsu da ke kar?ar haraji sun ci gaba da kar?ar tsoho da sabon ku?i. A wani sa?o da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce za a yi hakan ne bisa umarnin Kotun Kolin ?asar na ci gaba da amfani da tsofaffin ku?in ?asar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci. Haka kuma gwamnan ya ce dokokin jihar Kaduna sun haramta wa hukumomin gwamnatin jihar kar?ar haraji ku?i hannu. Sai…
Read MoreTallafin Mai Na Lashe Naira Biliyan 400 Duk Wata – NNPC
Kamfanin mai na NNPCL na ?asa ya ce adadin ku?in da ake biya a matsayin tallafin man fetur a kowanne wata ya haura naira biliyan 400. Kamfanin dillancin labaran ?asar NAN ya ruwaito shugaban kamfanin Mele Kyari na bayyana haka a Abuja babban birnin ?asar a lokacin kammala sauya wa kamfanin fuska.. Kyari ya ?ara da cewa kamfanin na NNPCL na kashe kusan naira 202 a matsayin tallafi ga kowacce litar mai a fa?in ?asar Ya kuma ce a kowacce rana kamfanin na samar da litar mai miliyan 65 domin…
Read MoreBabban Banki Ya Karyata Labarin Umartar Bankuna Da Karbar Tsoffin ?1000 Da ?500
Babban bankin Najeriya ya karyatq maganar cewa ya canza shawara kan lamarin mayar da tsaffin kudin N1000 da N500 ko wane bankuna Dubunnan yan Najeriya sun dira ofishohin CBN yau don mayar da tsaffin kudadensu bayan jawabin Buhari. Gwamnoni akalla 10 suka ja daga dashugaban kasa inda wasu suka fara yi masa bore Jawabin wanda har bankuna sun fara sanar da kwastamominsu su kawo kudi ya karade kafafenyada labarai. Har an ruwaito Daraktan Sadarwa na bankin, Osita Nwanisobi, da tabbatar da labarin. Kusan dukkan kafafen yada labaran Najeriya sun dauki…
Read MoreKarancin Kudi: Gwamnan Neja Ya Bi Sahu Wajen Maka Buhari Kotu
Gwamnatin jihar Neja ta shigar da karar gwamnatin tarayya a dalilin tsarin da bankin CBN ya fito da shi na canza wasu takardun kudi, Neja ta zama jiha ta biyar da za tayi shari’a da gwamnatin Muhammadu Buhari a kan tsarin kudin. Kwamishinan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin jihar Neja, Nasara Danmallam ya fitar da jawabi cewa sun kai kara gaban koli, yana cewa kararsu mai lamba SC/CV/210/2023 tana kotun koli tun a ranar Juma’a, su na sa ran a biya masu bukata. Kwamishinan ya ce su na rokon babban…
Read MoreZa A Wadata ‘Yan Najeriya Da Sabbin Takardun Naira – Babban Banki
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kamfanin buga kudin Najeriya (NSPM) ya bayyana cewa ya gama shirye-shiryen cigaba da buga sabbin kudin Najeriya da aka sauyawa fasali. Wannan ya biyo bayan labarin da ke yawo cewa babban bankin Najeriya CBN ya bayyana rashin isassun kayan aikin buga kudaden a masana’antar NSPM. Shugaban kamfanin, Ahmed Halilu, ya yi watsi da labarin inda yace suna da isassun kayan aikin buga sabbin kudi, hakazalika ya yi watsi da cewa kamfanin De-La-Rue na kasar Birtaniya ne ke bugawa Najeriya…
Read MoreMuna Fama Da Karancin Takardun Buga Sabbin Kudi – Gwamnan Banki
Labarin da ke shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar biyo bayan fama da ?arancin ku?i da ake fama dashi a Najeriya, Gwamnan Babban Banki ya yi bayani kamar haka “A halin yanzu, ana fama da karancin takardun da za a buga takardun kudi”. A wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, an ji Godwin Emefiele ya koka a kan yadda karancin takardu ya kawowa tsarin da ya kawo wa shirin illa. Gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito da tsarin takaita yawon kudi a al’umma, wanda hakan…
Read More