Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kamfanin buga kudin Najeriya (NSPM) ya bayyana cewa ya gama shirye-shiryen cigaba da buga sabbin kudin Najeriya da aka sauyawa fasali.
Wannan ya biyo bayan labarin da ke yawo cewa babban bankin Najeriya CBN ya bayyana rashin isassun kayan aikin buga kudaden a masana’antar NSPM.
Shugaban kamfanin, Ahmed Halilu, ya yi watsi da labarin inda yace suna da isassun kayan aikin buga sabbin kudi, hakazalika ya yi watsi da cewa kamfanin De-La-Rue na kasar Birtaniya ne ke bugawa Najeriya kudi inda yace ko takardu kamfanin bai sayarwa Najeriya.
“Kamfanin buga takardun kudin Najeriya watau Nigerian Security Printing and Minting (NSPM) ya samu labarin da ake nasabtawa gwamnan bankin CBN kan cewa kamfanin NSPM ba zai iya cigaba da buga sabbin kudi ba saboda rashin kayan aiki.”
“Bayan CBN ya yi watsi da wannan labari, muna son mu kara da cewa kamfanin De-la-Rue na Birtaniya bai bugawa Najeriya kudi hakazalika bai sayarwa kasar nan takardu.” “Muna son jaddadawa yan Najeriya cewa NSPM ya shirya komai don cigaba da buga takardun kudi bisa tsarin CBN na 2023.”
