Gwamnatin jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya umarci ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar da su tabbatar cewa hukumominsu da ke kar?ar haraji sun ci gaba da kar?ar tsoho da sabon ku?i.
A wani sa?o da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce za a yi hakan ne bisa umarnin Kotun Kolin ?asar na ci gaba da amfani da tsofaffin ku?in ?asar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci.
Haka kuma gwamnan ya ce dokokin jihar Kaduna sun haramta wa hukumomin gwamnatin jihar kar?ar haraji ku?i hannu.
Sai dai kawai hukumomin da gwamnatin jihar ta amincewa kar?ar garin ku?in, wa?anda su ma ya yi kira a gare su da su yi biyayya da hukuncin Kotun Kolin ?asar.
Gwamna El-Rufai dai na daga cikin gwamnonin da jihohinsu suka kai ?arar gwamnatin tarayya gaban Kotun Kolin ?asar bisa matakin sauya fasalin ku?in, tare da ?alubalantar daina amfani da tsofaffin takardun ku?in ?asar.
