Cire Tallafin Mai: Kamfanin NNPC Ya ?ara Farashin Man Fetur

Kamfanin man fetur na ?asa NNPC ya tabbatar da cewa ya ?ara ku?in litar mai a ?asar.

A wata sanarwa da ta kamfanin ya wallafa a shafinsa na twitter, kamfanin ya ce ya yi ?arin farashin domin yin daidai da halin da ake ciki.

Kuma ya ro?i afuwa kan wahalhalun da hakan zai iya haifarwa.

Hakan dai na zuwa ne bayan shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar, a lokacin rantsar da shi cewa gwamnati ta dakatar da tallafin.

Tun bayan furucin sabon shugaban ?asar ne aka fara ganin dogayen layuka a gidajen mai, yayin da kowane gidan mai ke sayar da man a farashi daban-daban.

Related posts

Leave a Comment