Muna Fama Da Karancin Takardun Buga Sabbin Kudi – Gwamnan Banki

Labarin da ke shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar biyo bayan fama da ?arancin ku?i da ake fama dashi a Najeriya, Gwamnan Babban Banki ya yi bayani kamar haka “A halin yanzu, ana fama da karancin takardun da za a buga takardun kudi”.

A wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, an ji Godwin Emefiele ya koka a kan yadda karancin takardu ya kawowa tsarin da ya kawo wa shirin illa.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito da tsarin takaita yawon kudi a al’umma, wanda hakan ya kawo zanga-zanga a wasu garurwa.

Da aka je taron majalisar magabata a fadar shugaban kasa, gwamnan babban bankin ya shaidawa mahalarta kamfanin buga kudi ya gamu da cikas.

Matsalar da kamfanin NSPM ta samu ta jawo an gagara buga sababbin kudin da za su maye guraben tsofaffin N200, N500 da ‘yan N1000 da aka karbe.

“Takardun kamfanin buga kudi sun kare balle a buga ‘Yan N500 da N1000. Kamfanin ya na jiran isowar takardu daga wani kamfanin Jamus da kuma De La Rue, amma an zaunar da su tun tuni, ba za a iya amsa bukatarsu yanzu ba.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa bankin na CBN ya umarci NSPM ya buga Naira miliyan 70 na sababbin kudi, kenan an iya buga Naira biliyan 126. Abin takaicin shi ne kamfanin kasar ya sanar da babban banki cewa ba zai iya buga wadannan kudi a halin da ake ciki ba, alhali ana kukan karancin Naira.

Related posts

Leave a Comment