Jami’an hukumar ya?i da cin hanci da hana yi wa tattalin arzi?in ?asa ta’annati sun kama tsohon ministan lantarki na Najeriya, Injiniya Saleh Mamman, wata majiya a ma’aikatar lantarki ta tarayya ta shaida wa BBC.
Kafofin ya?a labaran ?asar sun ce EFCC ta kama Saleh Mamman ne tun da sanyin safiyar Laraba inda suke ci gaba da tsare da shi a shalkwatar hukumar da ke Abuja.
Sun ce kamen na da ala?a da zargin almundahanar wasu ku?a?e kimanin naira biliyan 22.
Zuwa yanzu, ba a ji wani martani daga ministan ko wasu makusantansa ba.
Sai dai a cewar kafofin labaran Najeriya jami’an EFCC sun kama Saleh Mamman ne game da jerin bincike a kan zargin aiwatar da wasu ayyukan lantarki.
Rahotanni sun ce ana zargin sa da ha?a baki da wasu jami’ai a ma’aikatar lantarki wa?anda ke kula da asusun ajiyar ku?a?en ayyuka a tashoshin lantarki na Mambilla da Zungeru, don karkatar da ku?i naira biliyan 22, tare da rabawa a tsakanin su.
Kafofin ya?a labaran sun ce bincike ya banka?o wasu kadarori a Najeriya da ?asashe waje masu ala?a da jami’an da ake zargi, sannan an ba da rahoton gano miliyoyin nairori da daloli.
