Gwamnatin tarayya ta ce za ta mutunta umarnin da Kotun Kolin kasar ta bayar a kan karar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar inda kotun ta sa dakatar da aiwatar da wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na naira 200 da 500 da kuma 1,000 a yau 10 ga watan Fabrairu. A ranar Laraba ne dai kotun ta bayar da umarnin inda ta ce a dakata da amfani da wa’adin har zuwa ranar 15 ga watan na Fabrairu lokacin da za ta yanke hukunci a kan shari’ar da…
Read MoreCategory: Tattalin Arziki
Tattalin Arziki
Dangote Ya Bada Lakanin Maganin Talauci A Najeriya
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babban ?an kasuwa Aliko Dangote ya jajirce wajen ganin cewa an farfa?o da masana’antar sa?a a Najeriya. Da yake jawabi a taron shekara-shekara karo na 50 (AGM) na kungiyar masana’antun Najeriya (MAN) ya yi kira da a ?aure ‘yan Najeriya masu shigo da kayan masa?u daga ?asashen waje. A cewar attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, yana da muhimmanci majalisar dokokin ?asar ta zartar da wata doka da za ta hukunta sayar da kaya kasar waje ta…
Read MoreDa Dumi-Dumi: Kotu Ta Hana CBN Aiwatar Da Wa’adin Amfani Da Tsoffin Kudi
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotun ?olin ta tarayya ta dakatar da gamnatin Buhari daga aiwatar da wa’adin amfani da tsoffin takardun ku?in kasar. A baya dai CBN ya saka ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsoffin takardun 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sake. Jihohin arewacin ?asar uku ne dai da suka ha?ar da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da ?arar a gaban Kotun ?olin ?asar suna bu?atar kotun da…
Read MoreKotu Ta Hana Shugaban Kasa Da Gwamnan Banki Kara Wa’adin Amfani Da Tsoffin Kudi
Babbar Kotun Birnin Tarayya ta hana Shugaba Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kara wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira da aka sauya fasalinsu. Alkalin kotun, Mai Shari’a Eleoje Enenche ya kuma hana daukacin bankuna da ke Najeriya yin duk wata hulda da ta danganci tsoffin takardun kudin ko neman kara wa’adin amfani da su daga ranar 10 ga watan 10 ga watan Fabrairu da muke ciki. Da yake sauraron ?arar da wasu biyar daga cikin jam’iyyun siyasa 18 da ke Najeriya suka shigar, alkalin ya bukaci…
Read MoreDa Dumi-Dumi: Kotu Ta Bada Umarnin Garkame Shugaban EFCC
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotu ta yi umurnin garkame shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, a gidan gyara hali na Kuje kan kin bin umurninta. Jaridar Daily Independent ta ruwaito cewa, an umurci Sufeto Janar na Yan Sanda da ya tabbatar da kama Bawa tare da tsare shi a gidan yari nan da kwanaki 14 masu zuwa har sai ya wanke kansa daga zargin da kotu ke yi masa. Da yake yanke…
Read MoreKauyawa Sun Fi Kowa Shiga Wahala Kan Sauya Takardun Naira – El-Rufa’i
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya tsawaita wa’adin daina karbar tsoffin takardun kudi cewa lokacin ya yi gajarta da yawa, kuma jama’a na shan wahala sosai. Babban bankin Najeriya dai ya ce za a daina amfani da tsoffin kudade a kasar daga ranar 31 ga watan Janairu lamarin da ya jefa al’umma musamman talakawa a halin wayyo Allah. El-Rufai ya bayyana cewa mutanen karkara da dama wadanda basu da hanyar yin hada-hada kudi sune wadanda wannan hukunci zai fi shafa. Da yake jawabi…
Read MoreZa Mu Hukunta Bankuna Masu Bayar Da Tsoffin Kudi – CBN
Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa duk da wa’adin da babban bankin kasa CBN ya dauka na daina amfani da tsoffin kudade na matsowa, bankunan kasar nan ba sa zuwa karbar sabbin kudin da aka buga, a cewar babban bankin. CBN ya ce ya sha rokon bankunan kasar nan da su zo su dauki sabbin kudaden amma ba sa zuwa gaba daya maimakon haka suna cigaba da ba ‘yan Najeriya tsoffin ku?in. A shekarar 2022, CBN ya sanar da yin sabbin kudaden Naira da suka…
Read MoreMun Kwato Dala Miliyan 12 Daga Barayin Gwamnati – Gwamnatin Tarayya
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta ce ta yi nasarar ?wato dukiyar ?asar da wasu jami’an gwamnati suka sace a ku?a?en ?asar waje da suka ?unshi fan miliyan 6.3 da yuro miliyan 5.4 da dala 390,000. Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ce ana amfani da wasu daga cikin ku?a?en wajen aiwatar da wasu ayyuka kamar ginin hanyar Abuja zuwa Kano, da Legas zuwa Ibadan, da kuma ginin gadar Second Niger Bridge a yankin kudu maso gabas. Ministan ya bayyana hakan ranar Alhamis…
Read MoreBabban Banki Bai Buga Sabbin Kudi Ba Fenti Aka Yi Wa Tsofaffi – Gudaji Kazaure
?an Majalisar wakilai mai wakiltar ?ananan hukumomin Kazaure da Gwiwa a Jihar Jigawa Honorabul Gudaji Kazaure, ya fito fili ya kalubalanci buga sabbin takardun naira da CBN ke ikirarin yi inda yace karya ne ba a buga sabbi ba fenti kawai aka yi wa tsofaffin. Gudaji Kazaure ya kwarmata wannan magana a tattaunawar da gidan rediyon DW ya yi dashi akan cece kuce da ake yi akan sabbin takardun ku?in da bankin ya buga. ?an Majalisar ya ?ara da cewar a matsayin shi na kwararre wanda ya san yadda ake…
Read MoreDokar Kayyade Cire Kudi Ta Fara Aiki A Najeriya
A ranar Litinin 9 ga watan Janairun 2023 ne sabuwar dokar takaita cire kudi ta fara aiki a Najeriya tun bayan da aka bayyana sanya ta a shekarar da ta gabata. Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana a baya cewa, ya kirkiri hanyar rage yawaitar yawon kudade a hannun jama’a domin tabbatar da ana amfani da hanyoyin biya daban-daban. A dokar da CBN ya sanya, ya ce daidaikun mutane za su iya cire N500,000 ne a mako a bankuna ko injunan ciren kudi na ATM. Hakazalika, an ba kamfanoni damar…
Read MoreMun Buga Takardun Naira Fiye Da Bukatun ‘Yan Najeriya – CBN
Babban bankin kasa CBN ya yi watsi da rahotannin cewa ana samun karancin sabbin tsabar kudi a fadin bankunan Najeriya, Bankin ya ce akwai isassun kudi a bankuna a fadin kasa kuma yana kan bakan sa na daina amfani da tsaffin takardun dake yawo hannun mutane ranar 31 ga Junairu, 2023. Bankin ya kara da cewa shi bai hana bankuna baiwa mutane sabbin kudi a kan kanta ba kawai dai an umurci bankunan ne su kara adadin kudaden da suke zubawa a na’urar ATM saboda sabbin takardun suyi yawa hannun…
Read MoreBankin Najeriya Ya Umarci Bankuna Da Sanya Sabbin Naira A Na’urar ATM
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Bankin ?asa CBN ya umarci bankunan ?asar da su daina bayar da sabon ku?i ga kwastomomin da suka shiga cikin banki domin kar?ar ku?i. A maimakon haka babban bankin ya bu?aci bankunan da su saka sabbin ku?in cikin na’urorinsu na cirar ku?i na ATM. Domin tabbatar da cewa ku?in ya shiga hannun jama’a gabanin ranar wa’adin 31 ga watan da muke ciki da babban bankin ya saka na daina amfani da tsohon ku?in. Rahotonni sun ce babban bankin…
Read MoreEFCC Za Ta Yi Gwanjon Kadarorin Barayin Gwamnati
Hukumar EFCC ta sanar da cewa a ranar 9 Ga Janairu za ta yi gwanjon wasu kadarorin da su ka ha?a da manyan gidaje, filaye da fulotan da ta ?wato daga yawancin ?arayin gwamnati da kuma mazambata. Za a yi gwanjon kadarorin ne a ranar 9 Ga Janairu, 2023, a dandalin taron yaye ?alibai na Jami’ar NOUN da ke ma?wautaka da Hedikwatar EFCC. Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba. Haka nan kuma EFCC ta umarci dukkan masu son shiga…
Read MoreBarayi Sun Sace Gangar Mai Miliyan 17 A Najeriya
Wannan rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da karancin man fetur a sassan kasar. Wani sabon bincike da aka gudanar kan lamurran da ke wakana a fannin arzikin man Najeriya ya nuna cewar, an fitar da ganga sama da miliyan 17 na danyen mai daga kasar zuwa kasashen ketare ta barauniyar hanya, a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020. Rahoton da Andrew Ogochukwu Onwudili, babban jami’i mai binciken kudi na Najeriya ya fitar, ya kiyasta cewar kwatankwacin kudin danyen man fetur din da a iya cewa…
Read MoreMun Kashe Biliyan 10 Wajen Buga Sabbin Takardun Naira – Babban Banki
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mataimakiyar gwamnan CBN, Aisha Ahmed, ta bayyana cewa kudin da aka kashe kan buga sabbin kudi a shekara ya karu zuwa Naira Biliyan Goma N10bn. Aisha ta bayyana hakan ne ranar Juma’a yayinda da ta bayyana gaban majalisar wakilan tarayya a madadin gwamnan bankin, Godwin Emefiele. bayyana cewa kashi 90% na kudin da ake kashewa kan manajin Naira buga sabbin takardun kudi ake da su, babban bankin na kashe N150bn wajen buga sabbin kudi da lalata tsaffi a shekara.…
Read MoreMajalisar Wakilai Za Ta Yaki Dokar Takaita Cire Kudi
Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu ‘yan Majalisar Wakilan sun ci alwashin tilasata wa Babban Bankin ?asar (CBN) wajen dakatar da shirinsa na rage yawan adadin kudin da ‘yan ?asa da kamfanoni kan cira a kullum, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Wani daga cikin shugabanni a Majalisar ya fa?a wa jaridar cewa akasarinsu sun aminta cewa ya kamata a jingine dokar baki ?ayanta. A cikin sabuwar dokar, mafi yawan abin da mutum zai iya cirewa a mako na tsabar ku?i shi ne naira N100,000,…
Read MoreJanye Tallafin Mai Shi Ne Mafita A Najeriya – El-Rufa’i
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi hasashen manyan matsalolin da sabon shugaban Najeriya zai fuskanta inda ya kama aiki, El-Rufai ya ce dole ne wanda zai karbi mulkin kasar nan ya yi kokarin shawo kan matsalar tattalin arziki. Gwamna Nasir El-Rufai ya ce don haka akwai bukatar a magance matsalar tallafin man fetur da kuma tashin da kudin kasar waje suke yi a halin yanzu. Gwamnan na Kaduna ya ce idan shugaban kasar da aka zaba ya yi…
Read MoreMun Karbo Naira Biliyan 30 A Hannun Dakataccen Akanta Janar
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ya ce zuwa yanzu an karbe N30bn daga hannun Idris Ahmed tsohon Akanta Janar na ?asa. Wadannan biliyoyi su na cikin N109bn da ake zargin Idris Ahmed ya karkatar a lokacin yana rike da ofishin Akanta Janar na kasa. Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa ya shaidawa Duniya wannan a lokacin da ya halarci wani taro da aka yi da manema labarai a birnin tarayya Abuja.…
Read MoreTakaita Cire Kudi Zai Rage Wa ‘Yan Siyasa Sharholiya – Sanusi
Khalifa Muhammad Sanusi , ya ce matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na takaita cirar kudaden zai fi yin tasiri a kan `yan siyasa kasar fiye da talakawa. Ya bayyana hakan ne a karshen karatun Madaris da ya saba yi duk karshen mako. Ya ce `yan siyasar kasar na amfani da kudi a lokacin zabe don sayen kuri’un jama’a, lamarin da ke haifar da koma-baya ga kasar. Muhammadu Sanusi na II ya ce “abin takaici ne yadda mutane za su yi shekara hudu suna kwasar dukiyar al’umma, suna barin…
Read MoreMun Tura Sabbin Takardun Naira Bankuna – Gwamnan Babban Banki
Gwamnan Babban Bankin ?asa, CBN, Godwin Emefiele, ya ce sabbin takardun kudi na Naira da aka canja wa fasali tuni sun isa bankuna kuma su na jiran a bada umarnin fara fitar da su. A cewar wata sanarwa da CBN ya wallafa a shafinsa na Twitter, Emefiele ya bayyana haka ne a Daura yayin da ya kai ziyarar yi wa shugaban kasa Muhanmadu Buhari karin bayani kan sake fasalin kudin Naira da kuma manufar hada-hadar ku?i ta hanyar sadarwa da aka sake dawo da ita. Ya ce sake fasalin kudin…
Read More