Wa’adin Tsoffin Kudi: Ba Mu Saba Umarnin Kotu Ba – Ministan Shari’a

Antoni Janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami a ranar Alhamis ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai saba umurnin kotun koli ba kan batun wa’adin daina amfani da tsaffin kudi da wasu gwamnonin jihohi suka yi kararsa.

Malami ya ce idan dai doka ake magana, akwai zabi daban-daban, ya yi wannan jawabin ne a wurin taron ministoci karo na 67 da aka yi a gidan gwamnati a ranar Alhamis.

A ranar 8 ga watan Fabrairu ne kotun kolin ta bada umurni na hana babban bankin kasa, CBN, bada wa’adin daina amfani da tsaffin N200, N500 da N1000. Kotun ta bada umurnin ne biyo bayan karar da gwamnonin jihohin arewa guda uku – Kogi, Kaduna da Zamfara suka shigar.

Duk da umurnin kotun, Shugaban kasar a jawabin da ya yi a ranar 16 ga watan Fabrairu, ya ce ya umurci CBN ya raba wa al’umma tsohon N200, ya kuma ayyana tsaffin N500 da N1000 a matsayin haramtattun kudi.

Umurnin na shugaban kasa ya saba abin da kotun koli ta furta na cewa a cigaba da amfani da tsaffin takardun nairan har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan karar da gwamnonin jihohi suka shigar. Jawabin na shugaban kasa ya janyo suka daga wasu yan Najeriya da ke ganin shugaban kasar ya saba umurnin kotun koli.

Malami ya ce: “Gaskiyar ita ce, karara, ba mu saba wa duk wani umarni da kotu ta bayar ba, har da duk wani umarni da ya shafi sake fasalin naira. Ba mu saba doka ba.

Related posts

Leave a Comment