Tallafin Mai Na Lashe Naira Biliyan 400 Duk Wata – NNPC

Kamfanin mai na NNPCL na ?asa ya ce adadin ku?in da ake biya a matsayin tallafin man fetur a kowanne wata ya haura naira biliyan 400.

Kamfanin dillancin labaran ?asar NAN ya ruwaito shugaban kamfanin Mele Kyari na bayyana haka a Abuja babban birnin ?asar a lokacin kammala sauya wa kamfanin fuska..

Kyari ya ?ara da cewa kamfanin na NNPCL na kashe kusan naira 202 a matsayin tallafi ga kowacce litar mai a fa?in ?asar

Ya kuma ce a kowacce rana kamfanin na samar da litar mai miliyan 65 domin wadata ?asar da man fetur.

Shugaban kamfanin ya ce kamfanin zai ci gaba da yin abin da ya wajaba a kansa na samar wa ‘yan ?asar man da suke bu?ata.

Yana mai cewa biyan sama da naira biliyan 400 a kowane wata a matsayin tallafin man na matu?ar yin tarna?i ga harkokin ku?in kamfanin.

Ya ci gaba da cewa, kamfanin na NNPCL shi ne ka?ai kamfanin da ke shigar da mai cikin ?asar, kuma zai ci gaba da taka rawa cikin shekaru masu zuwa duk da yawan ku?in tallafin da yake biya.

Mele Kyari ya ce ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun daina shigar da mai cikin ?asar sakamakon wahalar da suke fuskanta wajen samun Dalar Amurka da ake bu?ata domin shigar da man zuwa ?asar.

Related posts

Leave a Comment