Taraba: Gwamna Ya Haramta Hako Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba

DAGA BASHIR ADAMU, JALINGO

Rahotannin dake shigomana yanzu daga Jihar Taraba na cewa, Gwamna Dr. Agbu Kefas ya haramta hako ma’adinan Kasa a dukkanin fadin Jihar.

Gwamnan ya fadi hakanne lokacin da yake ganawa da Sarakunan Gargajiyan Jihar, a Gidan Gwamnati dake Jalingo. Inda ya umurci Sarkunan a matsayin su na Iyayen Kasa, ya zama wajibi gwamnati ta hada kai dasu wajen kawo karshen matsalar tsaron da Jihar ke fama dashi.

“Jihar Taraba kamar sauran Jihohi dake Kasannan, na fama da matsalolin rashin tsaro da ya kunshi, Yan Fashin Daji, yin garkuwa da mutane domin karban kudin fansa, rikicin Kabilanci da rikicin Manoma da Makiyaya, dake haifar da azabar wahala ga Al’ummar mu.

“Salwantar rayukan da basuji ba basu ganiba, tarwatsa Mutane a garu-ruwansu da barnata dukiyoyinsu ya haifar da mummunar illa ga kyak-kyawar zamantakewar Jihar mu. Ya zama wajibi mu hada kai baki dayanmu, muyi ma kanmu tukka ga wadannan matsalolin, mu dawo da zaman lafiya da tsaro a Jihar mu.

“Ya ku masu Martaba, na umurce ku duka, kuyi anfani da martaban ku, ku hada kan Jama’a baki daya da fahimtar juna, da tabbatar da zaman lafiya daga matakin farko na Unguwanni domin daukaka darajan Jihar.

“Ya ku masu Martaba kuma Iyayen Kasa, na jadda da matsaya matuka, tare da jan hankalinku kan yanda yawaitan hakkan ma’adinai ba bisa ka’ida ba yayi kamari a Jihar. Wanda kuma ko shakka babu bangaren Ma’adinai nada matukar tasiri a taswiran kawo cigaba, kuma rikon sakainar kashi a bangaren, na haifar da illa ga kasanmu, tattalin arziki da ma al’adunmu na yau da kullum, tare da haifar da zai-zayan Kasa da dumaman yanayi, haifar da illoli ga lafiya da dai-daita garuruwa.

“A saboda haka ya zama wajibi mu kawo karshen aikata ire-iren ababen rashin ka’ida a fadiin Jihar mu Taraba.

Related posts

Leave a Comment