Kano: Zan Cigaba Da Bincikar Faifan Bidiyon Dalolin Ganduje – Muhuyi Rimin-Gado

Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci (PCACC) a jihar Kano, Muhuyi Rimingado ya sha alwashin ci gaba da binciken tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan batun zargin karbar cin hancin wasu daloli.

Muhuyi ya ce binciken zai ta’allaka ne akan badakalar Daloli da aka ga gwamnan a wani faifan bidiyo na karba daga wurin ‘yan kwangila yana durawa a aljihunsa.

Sabon Gwamna Abba Kabir a ranar Laraba 21 ga watan Yuni ya dawo da Muhuyi kujerarsa bayan dakatar da shi da tsohon Gwamna Ganduje ya yi a shekarar da ta gabata.

JaridarDaily Nigerian ta ce dakatarwar ba ta rasa nasaba da bincikar badakalar da Muhuyi ya ke yi akan wasu kwangiloli da tsohon gwamnan ya bai wa iyalansa.

Yayin da ya ke hira da ‘yan jaridu, Rimingado ya sha alwashin binciko badakalar Daloli da kuma dagewa wurin ganin ya dakile cin hanci a jihar. A cewarsa: “Na ji dadi yadda gwamnati ta bi umurnin kotu wurin dawo da ni kujerata, kuma na ji dadin yadda mutane suke turo sakon taya murna. “Hakan shi ya ke tabbatar da cewa mutane sun ji dadin aikin da muka yi a baya, kuma ina mai tabbatar da cewa zamu kara kokari sosai.”

“Kamar yadda na ce kafin a dakatar da ni, muna binciken bidiyon, kuma zamu ci gaba da binciken yanzu ma, duk sauran abubuwa da mutane suke tsammanin an manta da su zamu dawo mu ci gaba da bincikensu.” Ya ce duk da matsalolin da ya fuskanta a baya, ba zai gajiya ba don ganin ya kauda cin hanci a jihar.

Related posts

Leave a Comment