Gwamnatin Bauchi Ta Karbi Dala Miliyan Biyu Daga Bankin Duniya – Bala Mohammed

Daga Adamu SHEHU Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta karbi zunzurutu kudi na dalar Amurka miliyan biyu daga asusun Bankin duniya da zimmar kawar da matsalar ambaliyar ruwa da kuma zaizayar kasa da ya addabi kana nan hukumomimin Jihar baki daya,

Gwamnan Jihar Bala Abdulkadir Mohammed ne ya saida haka a lokacin wani zama na musamman da masu ruwa da tsaki na yankunan da wadan nan matsaloli sukafi ta gaiyyara wa a shekarun baya.

Taron ya gudana ne a dakin taron da ke yankin rundunar sojin kasa dake Bauchi, tare da kira ga wadanda aka zamo matsayin manzzanni da zasu tabbatar da shirin aikin ya isa zuwa ga sauran mutane a yanku nan karkara da suke fama da matsalar.

Shirin wanda asusun Bankin duniya zata tallafawa jihohin sha tara na myinda Jihar Bauchi tana daya daga wadanda zasu ci gajiyar kudin daya kai jimmilar dalar amurka miliyan dari bakwai 7 baki daya

“a madadin wadanda suka taimaka ganin wan nan kudirin jiha ya kankama don tabbatar da kawar da matsaloli ambaliyar ruwa da kwararowar hamada da ya addabi yankunan Jihar mu baki daya, munkarbi dalar amurka miliyan biyu somin tabi, bisa ga kokarinmu a matsayin gwamnatin Jihar Bauchi,

“Haka kuma, nayi matukar farin ciki da irin jajircewar da namijin kokarin shi shugaban shirin aikin, a fadin Jihar Dakta Kabiru Ibrahim” Ya jaddada

A wajen taron da yake jawabi a matsayin uban shirin tallafin a Jihar Bauchi Sarkin Katagum Umar Farouk na biyu, ya yabawa Gwamnan Jihar da kokarin sa bayar da kason Jihar a cikin shirin aikin kimanin naira miliyan biyar 5,

Yace zai tabbatar da anyi aiki tukuru don acimma abunda a kasa gaba, tare da kiran alummomin da matsalar ta shafa kai tsaye dasu taimaki gwamnati don aiwatar da aikin cikin natsuwa kuma kan kari.

Daga karshe shugaban chibiyar kare muhalli da rage radadin matsalar ta kasa
Ya karrama Gwamnan Bala a matsayin Jihar Bauchi tayi ma takwarorinta zarra ta wajen himma da kwazo akan shirin aikin tallafin bankin duniyar.

Related posts

Leave a Comment