Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya ce birnin Zariya na cikin tsaka mai wuya. Sarkin ya bayyana hakan ne a yau Litinin lokacin da ya kar?i ba?uncin tawagar Shugabannin Tsaro ?ar?ashin jagorancin Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samueal Aruwan. Sarkin ya ce mazauna bairnin ba sa samun barci da ido a rufe saboda sace-sacen mutane da ake yin don neman ku?in fansa a cikin birnin da kewayensa. Ya bayyana yanayin a matsayin wanda ba za a…
Read MoreCategory: Tsaro
Tsaro
Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Hari A Birnin Zazzau
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘Yan bindiga na ci gaba da cin karen su ba babbaka a Zariya da ke Jihar Kaduna inda suke kai hari wurare daban-daban a birnin suna sace mutane domin karbar kudin fansa. Ko a daren Asabar din da ta gabata, kimanin mutum 12 ne ’yan bindigar suka yi awon gaba da su a sabuwar unguwar da ke tsakanin Kofar Gayan da Kofar Kona a birnin Zariya. Majiyarmu ta ce mutane takwas aka sace a gida daya,yayin da aka bi gidaje biyar aka dauko…
Read MoreBam ?in Soji Ya Hallaka Mahalarta Daurin Aure A Jihar Neja
Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar a wani harin bam da jirgin rundunar sojin sama ya gudanar a yankin garin Genu, jihar Neja, yayi sanadiyyar mutuwar wasu da suka halarci ?aurin aure, yayin da wasu da dama suka Jikkata. Rahotanni sun bayyana cewa harin da jirgin ya?in ya kai ya kashe wasu makiyaya dake aikin satar shanu, kuma jirgin ya taso ne daga sansanin soji dake jihar Katsina. Sai dai an gano cewa ?aya daga cikin bam ?in da jirgin ya jefa ya dira a wurin taron murnar ?aurin…
Read MoreBoko Haram, ISWAP Da IPOB Dangin Juna Ne – Soyinka
Fitaccen marubucin nan Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana kungiyar IPOB a matsayin ?anwa ga Boko Haram. Soyinka ya bayyana haka ne duba da irin ?arnar da ‘yan IPOB ke yi musamman ma a yankin Kudu-maso-gabas inda su ke karkashe mutane da jami’an tsaro da lalata ofisoshin Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) da sauransu. Da ya ke tsokaci kan batun haramta Tiwita a Najeriya, Farfesan ya ce gwagwarmayar tsagerun IPOB ba halastacciya ba ce. Ya ce, “Ba na goyon bayan wa?anda suka ?uge da ?ona ofisoshin ‘yan sanda tare halaka jami’ansu,…
Read MoreMatsalar Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Dakatar Da Sarkin Zurmi
Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamna Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi daga Sarauta, An dakatar da Sarkin ne a bisa dalilin rashin tsaro dake addabar karamar hukumar ta Zurmi dake jihar Zamfara. Kuma Gwamnan ya nada kwamintin da zai aiwatar da bincike akansa bisa ga tuhume-tuhumen da ake yi masa akan matsalar rashin tsaron. Wannan dai shine Sarki na hudu da wannan gwamnati ta dakatar kenan. Shin kowace nasara aka taba samu game da dakatar da Sarakunan da ake yi bisa zargin su…
Read MoreHarin ‘Yan Bindiga Ya Tilasta Rufe Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Nuhu Bamalli
Hukumar Kwalejin Nuhu Bamalli da ke Jihar Kaduna ta sanar da rufe makarantar sakamakon harin ‘yan fashin daji da ya yi sanadiyyar kashe ?alibi da kuma sace wasu guda takwas. Da daren Alhamis ne ‘yan bindigar suka afka makarantar, inda suka kashe ?alibi sannan suka yi garkuwa da malamai biyu da kuma wasu ?aliban guda takwas. Mazauna yankin sun ce maharan sun dinga harbi a kan kowa da kowa domin korar mutane. Wata sanarwa da ofishin ya?a labaran kwalejin ya fitar ta umarci dukkan ?alibai da su zauna a gida…
Read MoreSanatocin Arewa Sun Yi Taron Lalubo Hanyar Magance Matsalar Tsaro
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar Sanatocin Arewa sun gudanar da wani muhimmin taro domin lalubo hanyar magance matsalar tsaro dake addabar yankin Arewa shekaru da dama. Shugaban kungiyar Sanatocin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya fadi hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan tattaunawan sirri daya gudana a Zauren majalisar. Ya ce: “Mun hadu ne a matsayin Sanatocin Arewa don nuna matukar damuwarmu kan kalubalen tsaro a kasar nan. Mun damu a matsayinmu na ‘yan Najeriya kuma a matsayinmu na’ yan Arewa kuma…
Read MoreGwamnatin Tarayya Ta Bayyana Aniyarta Na Daukar ‘Yan Sanda 10,000
Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa gwamnatinsa a halin yanzu tana kan aikin daukan sabbin Jami’an ‘yan sanda 10,000 domin inganta tsaron a dukkanin fa?in kasa. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis a jihar Legas yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar domin kaddamar da wasu ayyuka. “A halin yanzu muna kan daukan sabbin jami’an ‘yan sanda 10,000 domin karfafa tsaro a sassan kasar,” in ji Buhari. Ya kara da cewa, “Na…
Read MoreGreenfield: Babu Gaskiya A Labarin Kama ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Kaduna
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ?arkashin jagorancin Gwamna Nasiru Ahmad El Rufa’i ta musanta rahoton da ake ya?awa cewa an samu nasarar cafke ‘yan bindigan da suka sace ?alibai a jami’ar Grienfield dake jihar Kaduna. Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samul Aruwan, shine ya bayyana hakan a wani martani da ya yi kan rahoton kama yan bindigan. Mr Aruwan yayi maratanin ne a wani gajeren rubutu da yayi a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook ranar Laraba. Yayin da yake martani kan rahoton, Kwamishina Aruwan Yace: “Ina…
Read More‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sama Da Mutane 30 A Jihar Binuwai
Rahotanni daga Jihar Binuwai na bayyana cewar adadin mutanen da suka mutu sakamakon wani harin ?an bindiga a ?aramar hukumar Agatu da ke jihar Benue a tsakiyar Najeriya ya kai kusan 30, yayin da har kawo yanzu ake tsammanin samun ?arin wasu gawarwaki. Mutane da dama sun ?aurace wa garin da aka kai harin saboda fargabar abun da ka je ya zo, la’akari da yadda ake yawan samun hare-haren ramuwar gayya a ?aramar hukumar. Mahukunta sun ce ana ci gaba da neman masu hannu a harin don daukar matakin doka…
Read More‘Yan Bindiga Sun Sace Mata 60 Da Kone Gari Kurmus A Zamfara
Rahotanni daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar ‘yan fashin daji sun sace wasu mata kimanin 60 a cikin wani samame da suka kai kan wasu kauyukka jiya (Talata). A cewar wani ?an majalisar wakilan kasar daga yankin, an sace matan ne daga kauyen Manawa yayin da aka kashe mutane hudu a kauyukan Malele da Randa a Karamar Hukumar Maru. Hon. Shehu Ahmed S. Fulani dan majalisa mai wakiltar yankin da lamarin ya faru a majalisar wakillan Najeriya ya shaida wa BBC cewa garuruwa da dama ne ?an…
Read MoreDa ?umi-?umi: An Haramta Amfani Da Gilashin Mota Mai Duhu
Shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya IGP Alkali Baba Usman ya sanar da haramta sanyawa motoci ba?in gilashi mai duhu wato “Tinted” ga kowane mai amfani da mota koshi waye. IGP Alkali Baba Usman ya baiwa jami’an tsaron ?an sanda damar damke duk wanda suka sake kama motar sa dauke da ba?in gilashi mai duhu “Tinted” koshi waye. IGP Alkali a ranar yau litinin 7 ga watan Yuni 2021, ya ce ya zama dole a haramtawa motoci sanya bakaken gilasai “Tinted” kasancewar bincike ya tabbatar ana amfani dashi wajen satar mutane…
Read MoreShekau Ya Cancanci Kisane Shi Ya Sa Muka Kashe Shi – ISWAP
Rahotanni daga Jihar Borno na bayyana cewar Kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta bayyana dalilinta na kashe shugaban kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, Abubakar Shekau, inda tace ya cancanci kisane shi yasa ta kashe shi. A wani sakon cikin gida daga shugaban ISWAP, Abu Musab Albarnawi, wanda jaridar HumAngle ta samu a ranar Juma’a, ya ce Shekau ya kashe kansa ne bayan kin mika kai da yayi sakamakon kutsen da aka yi a maboyarsu a ranar 19 ga watan Mayun 2021. Shugaban ISWAP yace shugaban rikon kwarya na ISIS na Iraq…
Read MoreKisan ‘Yan Arewa – Ha?urinmu Ya ?are – Wamakko
Tsohon Gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta tsakiya Dr Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kakkausar suka ga kungiyar IPOB da kuma shugabannin kabilar Ibo na kudancin Nijeriya akan kisan ‘yan Arewa a kudu. Wamakko ya ce” Ku daina fakewa da ‘yan kungiyar IPOB kuna kashe mana al’umma, ku sani cewa ba za mu lamunci hakan ba”. “Hakurin da muke yi akan abubuwan da ake yi wa ‘yan Arewa a kudancin Najeria ya kare”. “Mun baiwa matasan mu na Arewa hakuri lokuta da dama akan abubuwan da ke…
Read More‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 88 Rana Guda A Jihar Kebbi
Rahotanni daga Jihar Kebbi na bayyana cewar ‘yan bindiga sun tafka mummunan ta’asa na kisan jama’a bayin Allah wadanda ba su jiba kuma basu gani ba, Hukumar yan sanda a jihar Kebbi a ranar Asabar ta tabbatar da kisan mutum 88 da tsagerun yan bindiga suka yi a karamar hukumar Danko/Wasugu na jihar Kebbi. Kakakin hukumar, Nafi’u Abubakar ya bayyana cewa wannan ya auku ne duk a ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ?asa NAN ya ruwaito. Yace an kashe su ne a hare-haren da aka kai garuruwa…
Read MoreZamfara: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Da Dama
Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun hallaka manoma 12 tare da raunata wasu tara a kananan hukumomin Magami da Bayani a jihar Zamfara a yammacin jiya Juma’a. Yan bindigan sun kuma sace dabbobi da wasu kayayyaki masu muhimmanci da a yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba. An ruwaito cewa ‘yan bindigan sun kai harin ne a lokacin da manoman ke aiki a gonakinsu suna kokarin sharar gona domin shirin aikin daminan bana. An kuma ruwaito cewa an birne mutanen 12 da aka kashe bisa…
Read MoreMun Da?ile Garkuwa Da Mutane Da Rijistar NIN – Pantami
Dr Isa Pantami, ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani, ya ce bullo da NIN ya rage garkuwa da mutane da harin yan bindiga – Pantami ya yi wannan ikirarin ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da ya ke bayanin nasarorin da ma’aikatarsa ta samu tun fara aikinsa a 2019. Kamar yadda kamfanin yada labarai na Legit Hausa ya rawaito, Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Dr. Isa Pantami ya yi ikirarin cewa tsarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bullo da shi na tursasawa yan Nigeria mallakar lambar…
Read MoreAkwai Barazanar ‘Yan Bindiga A Jihar Kano – Ganduje
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun fara mamaye dazukan jiharsa kuma akwai yiwuwar suna shirin kai hare-hare ne, a ?auyuka da garuruwan Jihar ta Kano nan bada jimawa ba. Gwamnan ya yi wannan furucin ne a Hedkwatar Tsaro dake babban birnin tarayya Abuja inda ya gana da shugabannin sojoji, ya ce ‘yan bindigan na taruwa a dajin Falgore duk da jihar na kokarin bude dazukan. Duk da cewa ya bada tabbacin gwamnatinsa da…
Read MoreLokaci Ya Yi Da Za A Fara Tura Masu Yi Wa Kasa Hidima Filin Daga – Shugaban NYSC
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar NYSC ta masu yan yi wa kasa hidima, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya ce masu yi wa kasa hidimar suna cikin jami’an tsaron Nijeriya kuma ana iya basu horon zuwa yaki idan bukatar hakan ta taso. Janar Ibrahim ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da aka yi da shi a ranar Laraba yayin da ya ke magana kan batun kiraye-kirayen da wasu ke yi na cewa a soke tsarin yi wa kasa hidimar. Ya bayyana cewa irin horaswar da…
Read MoreKu Kashe Duk Wanda Aka Kama Da Makami A Zamfara – Matawalle Ga Jami’an Tsaro
Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamna Bello Matawalle na jihar ya umarci dukkan mazauna jihar da su mika makaman da suka mallaka ba bisa ka’ida ba ga hukumar ‘yan sanda mafi kusa dasu a cikin kwanaki bakwai kacal. Gwamnan ya bada wannan umarnin ne yayin saka hannu a wata takardar shela ga dukkan jihar Zamfara, kamar yadda hadiminsa a harkar yada labarai, Zailani Bappa ya sanar a ranar Laraba. Kamar yadda takardar ta nuna, umarnin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bada na…
Read More