Akwai Barazanar ‘Yan Bindiga A Jihar Kano – Ganduje

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun fara mamaye dazukan jiharsa kuma akwai yiwuwar suna shirin kai hare-hare ne, a ?auyuka da garuruwan Jihar ta Kano nan bada jimawa ba.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a Hedkwatar Tsaro dake babban birnin tarayya Abuja inda ya gana da shugabannin sojoji, ya ce ‘yan bindigan na taruwa a dajin Falgore duk da jihar na kokarin bude dazukan.

Duk da cewa ya bada tabbacin gwamnatinsa da hukumomin tsaro za su cigaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar, gwamnan yayin ganawa da babban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya roki sojojin su yi gaggawar aikin kafa sansanin horas da sojoji a dajin Falgore don sojoji su karbe dajin.

Ganduje ya ce zaman lafiyar da ake samu a jiharsa ta samu ne bisa kyakyawar alaka da ke tsakanin gwamnatinsa da hukumomin tsaro.

A cewarsa, “Na kawo ziyara ne don jajantawa sojoji bisa rasuwar tsohon shugaban Hafsan sojojin kasa Laftanat Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami’ai 10. Abu ne mai ciwo amma munyi tawakkali duba da cewa sun rasu ne yayin yi wa kasarsu hidima.

Na kuma zo nan ne don neman taimakon Rundunar Sojojin Nijeriya wurin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano; yan bindiga sun mayar da wasu dazukan jihar mabuyarsu.

“Muna gina gidaje, makarantu da asibitoci domin makiyaya a wasu dazukan amma duk da haka muna son sojoji su fara aiki a dajin Falgore.”

A jawabinsa, babban hafsan sojojin na kasa, ya yi alkawarin zai ziyarci dajin Falgore domin ganin yadda za a cigaba da ayyukan sojoji a dajin. Ya ce rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro za su cigaba da ganin sun dakile kallubalen tsaro a kasar.

Related posts

Leave a Comment