Sanatocin Arewa Sun Yi Taron Lalubo Hanyar Magance Matsalar Tsaro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar Sanatocin Arewa sun gudanar da wani muhimmin taro domin lalubo hanyar magance matsalar tsaro dake addabar yankin Arewa shekaru da dama.

Shugaban kungiyar Sanatocin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya fadi hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan tattaunawan sirri daya gudana a Zauren majalisar.

Ya ce: “Mun hadu ne a matsayin Sanatocin Arewa don nuna matukar damuwarmu kan kalubalen tsaro a kasar nan. Mun damu a matsayinmu na ‘yan Najeriya kuma a matsayinmu na’ yan Arewa kuma ba za Mu cigaba da zuba Ido ba.

Muna son kowane dan Najeriya ya yi Bacci Ido a rufe. “Dole ne mu nemi mafita. Mun damu ganin cewa duk yankunan-siyasa na ?asar suna Fuskantan ?alubalen tsaro daban daban. Dole ne mu nemi mafita ”.

Mun fara tattaunawa kan kalubalen tsaro kuma za mu ci gaba idan muka dawo daga hutu, in ji Wamakko.

Related posts

Leave a Comment