Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Hari A Birnin Zazzau

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘Yan bindiga na ci gaba da cin karen su ba babbaka a Zariya da ke Jihar Kaduna inda suke kai hari wurare daban-daban a birnin suna sace mutane domin karbar kudin fansa.

Ko a daren Asabar din da ta gabata, kimanin mutum 12 ne ’yan bindigar suka yi awon gaba da su a sabuwar unguwar da ke tsakanin Kofar Gayan da Kofar Kona a birnin Zariya.

Majiyarmu ta ce mutane takwas aka sace a gida daya,yayin da aka bi gidaje biyar aka dauko sauran.

Wata ganau, kuma diya ga daya daga cikin mutanen da aka sace, Hafsat Habib Kusfa, ta ce ’yan bindigar sun shiga gidan nasu ne da misalin karfe 12 na dare inda suka rinka bi daki-daki suna fito da mutane suna jera su a tsakar gida.

Ta bayyana cewa lokacin da suka shiga gidan na su, ’yan bindigar suna dauke ne da bindigogi da adduna kuma suna magana ne da harshen Fulatanci da Hausa lokacin da za su yi magana da mutanen da suka sacen.

Ta kara da cewa, bayan yin gardama a tsakanin su, sai suka ce mata ta koma gida domin ta kula da kananan yara da kishiyar mahaifiyar ta da ke jego.

“Mun kuma ga wasu daga cikinsu sun fito da wasu mutane, galibin su maza daga gidajen makwabta inda suka tafi da su.

“’Yan bindiga bakwai ne suka shiga gidanmu wadanda na gansu da ido na, kuma akwai biyu daga cikinsu a waje da basu wuce shekara 30 ba, sai wasu da suke tsakanin shekara 15 zuwa 20,” a cewar Hafsat.

‘An sako iyayena daga bisani’

Har ila yau, Hafsat ta ce ranar Lahadi da safe ’yan bindigar sun sako mahaifinta da mahaifiyarta inda aka kai su asibiti domin duba lafiyar su kasancewar duk basa iya magana.

“Lokacin da suka dawo alamu sun nuna cewa sun sha duka a wurin ’yan bindigar,” kamar yadda ta bayyana.

Wasu rahotannin da ba a tabbatar ba sun ce ’yan bindigar sun kuma sace wani tsohon Manajan Banki a gidansa da ke Anguwar Graceland da ke Kwangila a Zariya a daren Juma’a da karfe misalin karfe tara na dare.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace basu tantance yawan mutanen da aka dauke ba.

Related posts

Leave a Comment