Gwamnatin Neja Ta Yi Ko Oho Da Halin Da Dalibanmu Ke Ciki – Shugaban Islamiyyar Da Aka Sace Dalibai

Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar Alhaji Abubakar Hassan, mamallakin Islamiyyar Salihu Tanko dake garin Tegina a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, ya ce har yanzu gwamnati bata tuntubi hukumar makarantar ba saboda sace daliban da aka yi. A wani sakon murya da aka turawa manema labarai a ranar Laraba, Alhassan yace masu garkuwa da mutanen sun tuntubesu inda suka bukaci kudin fansa har naira miliyan dari. “Har yanzu gwamnati bata shiga cikin lamarin ba. Sakataren gwamnatin jihar ya tuntubemu ta bakin matarsa saboda muna da alaka da…

Read More

Muna Goyon Bayan ACF Na Hana ‘Yan Arewa Shiga Jihohin Inyamurai – Matasan Arewa

Kungiyar cigaban Matasan Arewacin Najeriya ta nuna goyon bayanta dangane da kiran da kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta yi na hani ga ‘yan Arewa shiga Jihohin Inyamurai sakamakon matsalar tsaro. ?aya daga cikin shugabannin kungiyar Alhaji Imrana Nass ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna. Imrana Nass ya ce ai tun asali ya kamata ace Dattawan sun yi wannan kiran ba a yanzu ba, domin halin da ‘yan Arewa ke ciki yanzu a Kudancin Najeriya abin tsoro da tashin hankali…

Read More

Filato: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda

Rahotanni daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ?auke da muggan makamai sun bindige wani mataimakin Kwamishinan ‘yan Sanda har lahira da tsakiyar ranar yau Laraba. ‘Yan Bindigar sun kashe Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda na kasa mai ritaya AIG Christopher Dega a birnin Jos na Jihar Filato da sanyin safiyar yau. ‘Yan bindigar sun dinga zazzaga masa albarusai ne a kirji har sai da ya ce ga garin ku nan. Wannan dai shine karo na hudu a jere da ‘yan bindiga suke kashe manyan mutane…

Read More

An Na?a Kingibe Jakadan Tafkin Chadi

Shugaba Muhammadu Buhari ya na?a Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babagana Kingibe mu?amin Jakada na Musamman a Chadi da Yankin Tafkin Chadi. Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja. “An na?a wannan mu?amin ne biyon bayan ?udirorin da aka cimma a taron Kasashen Yankin Tafkin Chadi kan Makomar Kasar Chadi, wanda aka gudanar a ranar 25 Ga Mayu. “Aikin Jakada na Musamman a Chadi da Tafkin Chadi, shi ne kula da lamurran da ke faruwa a Chadi da Yankin…

Read More

Ban Da Lokacin Barci Sai Na Ga Bayan ‘Yan Ta’adda – Shugaban Dakarun Soji

A ranar Litinin, sabon shugaban Hafsan sojin Najeriya Janar Faruku Yabaya ya bayyana cewa a yanzu baida wani buri da ya wuce ganin ya hallaka ‘yan ta’adda a kowace kusurwa ta Najeriya. Janar Faruku Yahaya ya bayyana hakan ne a yau Litinin a lokacin da ya kira taron manya Hafsoshin sojin Najeriya ne domin fuskantar matsalolin tsaro da Najeriya take ciki. A cikin jawabin sa, Janar Faruku Yahaya ya yi kira ga manyan Hafsan sojin Najeriyar da su tashi tsaye haikan don ganin an magance matsalar tsaro a kowace kusurwa…

Read More

Gwamnatin Zamfara Ta Sauke Sarkin ?ansadau

Gwamna Bello Mohammed (Matawallen Maradun, Barden Hausa, Shattiman Sakkwato) ya Amince da dakatar da Sarkin Dansadau, Alhaji Hussaini Umar da gaugawa. Kazalika Gwamnan ya Amince cewa Hakimin Dansadau, Alhaji Nasiru Muhammad S/Kudu da ya cigaba da kulawa da ayyukan Masarautar Haka nan kuma an sakatar da Hakimin Nasarawa Mailayi Alhaji Bello Wakkala da gaugawa, Gwamnan ya kuma kafa Kwamiti Mai ?arfi da zai binciki wadanda aka dakatar daga Mu?aman nasu. Shugaban wannan Kwamitin dai shine mai ritaya DIG Muhammad Ibrahim Tsafe, sai membobin Kwamitin da suka ha?a da Hon. Yusuf…

Read More

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Magatakardan Hukumar NECO

Rahotannin dake shigowa manema labarai ta hanyar Matar wanda aka kashe tace; wadansu ‘yan bindiga sune suka kashe Maigidan na ta wanda kafin a kashe shi shi ne magatakardar Hukumar shirya jarabawar kammala Sakandare ta kasa, NECO, wato Farfesa Godswill Obioma. Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai masa hari ne a daren ranar Litinin a gidansa, inda suka shake shi wanda matarsa ta bayyana kisan na shi a matsayin kisan kai. Da safiyar yau Talata ne matarsa, Elizabeth Obioma ta shaidawa manema labarai ta wayar tarho cewa wadanda suka…

Read More

Madugun ‘Yan Zanga-Zanga Sowore Ya Sha Harsashi A Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ‘Yan sanda a babban birnin sun harbi mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma tsohon dan takarar shugaban kasa yayin wata zanga-zanga a bakin Unity Fountain dake a Abuja. An harbi Sowore a gefen dama a cinya lamarin da ya sa aka yi gaggawan wucewa dashi asibiti domin ceto ranshi. Madugun ‘yan Zanga-Zangar ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa: “Yanzun nan ‘yar sanda, ACP Atine ta harbe ni a Unity Fountain a Abuja. Zanga-Zangar #RevolutionNow Yanzu aka fara gwagwarmaya za ta ci gaba…

Read More

Matsalar Tsaro: Gwamnan Neja Ya Kauracewa Jihar

Rahotanni daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnan Jihar ya lula ?asar waje, lokaci ka?an bayan kwashe ?aliban Islamiyya da ‘yan bindiga su ka yi, a Tegina, cikin ?aramar Hukumar Rafi. Sai dai kuma Kakakin Ya?a Labarai ta Gwamnan, Mary Noel-Berge ta ce ya tafi laluben hanyoyin da zai ?arfafa tsaron jihar ne. Sannan kuma ta ce ya tafi ne tun kafin a sace yaran. Ta ce Gwamnan ya tabbatar wa iyayen yara cewa ana nan ana ?o?arin ganin an ?wato ko an ceto yaran na Tanko…

Read More

Rundunar Soji Ta Kori Jami’anta 3,040 Daga Bakin Aiki

Rundunar Sojin Kasa ta kori kimanin sojoji 3,040 sakamakon laifuka da dama, da suka hada da rashin ladabi, sayar da miyagun magani da fyade gami da kisa. Wasu daga cikin sojojin, an sallame su ne, sakamakon kama su da laifin takardun bogi da rashin aiki tukuru, da fashin zuwa wajen aiki, gami da rashin gudanar da aikin Soji yadda ya kamata. Haka Zalika, wasu Kuma an same su da Matsalar Shekaru, da sata, da Kuma yunkurin yin fyade gami da sakin masu laifi ba bisa ka’ida ba. Kimanin Sojoji 1000…

Read More

Imo: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Kakakin Majalisar Jihar Adamawa Ahmad Gulak

Tsohon, Kakakin majalisar Dokokin jihar Adamawa,kuma tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan siyasa, Ahmed Gulak ya gamu da ajalin sa a Owerri, babban birnin jihar Imo ranar Asabar. An ruwaito cewa ‘mayakan kungiyar Tsageran Inyamurai, IPOB ne suka bindige shi a hayar sa ta zuwa filin jirgi daga dakin Otel din sa. Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa da ma kuma akwai wani bidiyo da aka samu dake bayyana sakon shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ya na gargadin duk wani mazaunin garin Owerri kada ya fita waje…

Read More

Da ?umi-?umi: ‘Yan Bindiga Sun Saki Daliban Jami’ar Greenfield Dake Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sako daliban jami’ar Greenfield bayan sama da wata guda a hannunsu cikin dokar daji. A rahoton gidan talabijin na Channels ya bayyana cewar dalibai 14 aka sake ranar Asabar din nan da muke ciki. Shugaban kungiyar iyayen daliban, Markus Zarmai da wasu sun je tarban daliban inda ‘yan bindigan sukayi alkawarin ajiyesu. An tuntubi Kakakin Rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, kuma ya tabbatar da wannan labari. A cewarsa, har yanzu yana neman bayani…

Read More

Sabon Shugaban Dakarun Soji Ya Shiga Ofis

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sabon Shugaban Dakarun Soji Manjo Janar Farouq Yahaya a ranar Juma’a 28 ga Mayu, ya fara aiki a matsayin Shugaban Sojojin Najeriya na 22 a Hedikwatar Soji da ke Abuja. Ya fara aikinsa ne cikin zimma ta hanyar duba masu tsaron Kwatas da duba sauran muhimman bayanan tsaron ?asa. A ranar Alhamis 27 ga watan Mayu ne hedikwatar tsaron ta sanar da nadin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Yahaya a matsayin sabon Shugaban Dakarun Sojin. Sabon Shugaban Dakarun Sojin…

Read More

Zamfara: An Gudanar Da Zanga-Zanga Da Gawawwakin Mutane

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar Zanga-zanga ta barke a safiyar ranar Juma’a a garin Zurmi, hedkwatar karamar hukumar Zurmi saboda yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da ke kashe mutane a garuruwa kamar Kaji a kullum. An ruwaito cewa Mutane da dama sun rasa rayyukansu wasu daruruwan sun rasa muhallansu sakamakon hare-haren yan bindiga da ya ki-ci ya-ki-cinyewa a garuruwan jihar. A makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun kai hari a wani gari a karamar hukumar Zurmi inda suka kashe fiye da mutane 11. Mazauna garin sun shaidawa majiyarmu…

Read More

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Masu Yawa

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar aikewa da wasu tulin ‘yan bindiga lahira, sannan ta samu nasarar cafke wasu 16 tare da kwato shanun da suka sace a jihar. Yan sandan sun kuma kwato wani adadi na miyagun ?wayoyi daga hannun yan bindigan. Kakakin hukumar yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isa, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Laraba. Isah yace an kama yan bindigan ne lokacin da sukayi artabu tsakanin yan sanda da yan bindigan a…

Read More

An Yi Allah Wadai Da Yunkurin Halasta Shan Tabar Iblis A Najeriya

Shugaban hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi, NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ya yi gargadin cewa yunkurin da wasu ke yi na ganin an halasta amfani da Tabar Iblis wato wiwi a Najeriya zai janyo wa kasar koma baya a nasarar da ta samu wurin yaki da sha da safarar muggan kwayoyi. Marwa ya yi wannan gargadin ne yayin jawabinsa wurin taron tsaro da majalisar wakilai ta kasa ta shirya a ranar Laraba a zauren Majalisar dake babban birnin tarayya Abuja. A cewarsa, akwai kwakwarar alaka…

Read More

Sokoto: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Basarake Da ‘Yan Banga 21

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Mahara sun kashe ‘Yan banga 21 da wani wani Dagaci a hari da suka kai wa Kauyen Yartsakuwa da ke karamar hukumar Rabah, jihar Sokoto. ‘Yan bindigan sun kashe Dagacin Sabon Birni ranar Talata ne bayan sun tare hanyar Sabon Birni zauwa Shinkafi, inda suka yi wa matafiya da dama fashin kaya da miliyoyin kudi da shanu masu yawa. Gwaman jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya ziyarci garin inda ya jajanta wa yan uwa da iyalan yan bangan da maharan suka kashe. Tambuwal ya…

Read More

Kawar Da Talauci Ne Maganin Matsalar Tsaro A Najeriya – Okorocha

Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, yace matu?ar ba’a magance talauci da rashin adalci a Nijeriya ba, to babu wani makami da zai yi nasara a ya?in da ake da rashin tsaro a ?asar nan. Okorocha, wanda ya yi jawabi a wajen taron shekara-shekara na 2021 NBA, mai taken “Rawar da mutane zasu iya takawa a gwamnatin Najeriya’, yace akwai dangantaka tsakanin talauci da rashin adalci. Sanatan ya kuma yi fatan Nijeriya za ta cigaba da kasance wa tsintsiya ?aya duk kuwa da kiraye-kirayen a raba ?asar da wasu…

Read More

An Kafa Kwamitin Bincikar Jiragen Sojin Najeriya

Babban hafsan sojan sama na Najeriya (CAS), Air Marshal Oladayo Amao ya kafa wani kwamiti na musamman da ya ?unshi har da manyan tsoffin sojojin da suka yi ritaya don gudanar da binciken lafiyar jiragen soji na ?asar da kuma ?angaren masu kula da su. Sanarwar da kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar a ranar Talata ta ce aikin kwamitin ya shafi binciken rahoton lafiyar jiragen sojin da ayyukan injiniyanci tare da ba da shawarar matakan inganta ayyuka da amincinsu. “Kwamitin ?ar?ashin jagorancin Air…

Read More

Majalisa Na Duba Yiwuwar Soke Yin Bautar Kasa A Najeriya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Wakilai na duba yiwuwar dakatar da shirin bautar Kasa na NYSC, Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya na Canji shekarar 2020, wanda ke neman soke dokar NYSC, an gabatar da shi a karatu na biyu a gaban majalisar. Wanda ya dauki nauyin yunkurin, Mista Awaji-Inombek Abiante, a cikin bayanin shawarar, ya zayyana dalilai daban-daban da za su sa a soke NYSC. “Wannan kudirin yana neman a soke Sashi na 315 (5) (a) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, 1999, (kamar yadda…

Read More