Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Aniyarta Na Daukar ‘Yan Sanda 10,000

Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa gwamnatinsa a halin yanzu tana kan aikin daukan sabbin Jami’an ‘yan sanda 10,000 domin inganta tsaron a dukkanin fa?in kasa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis a jihar Legas yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar domin kaddamar da wasu ayyuka.

“A halin yanzu muna kan daukan sabbin jami’an ‘yan sanda 10,000 domin karfafa tsaro a sassan kasar,” in ji Buhari. Ya kara da cewa, “Na umurci hukumar kula da albashi na kasa ta kara wa yan sanda albashi da alawus-alawus.”.

Kazalika, Shugaba Buhari ya ce tun shekarar 1999 babu wata gwamnati da ta tabuka irin kokarin da gwamnatinsa ta yi wurin kawo sauye-sauye a rundunar ‘yan sanda da tsarin tsaro a kasar. Bugu da kari, shugaban kasar ya lissafa wasu dokoki da ya rattaba hannu a kai tun hawarsa mulki wadanda suka shafi walwala da jin dadin yan sanda da inganta ayyukansu.

Wasu daga cikinsu sun hada da dokar asusu na musamman na walwala da samarwa ‘yan sanda kayan aiki da ya rattaba hannu a kai a 2019 da kuma yi wa dokar kafa ‘yan sanda kwaskwarima a 2020.

Daga karshe, Buhari ya yabawa gwamnan jihar Legas kan samarwa ‘yan sanda sabbin kayan aiki da zai taimaka musu wurin yaki da bata gari da tabbatar da doka da oda musamman bayan barnar da aka yi musu yayin zanga-zangar EndSARS.

Related posts

Leave a Comment