Shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya IGP Alkali Baba Usman ya sanar da haramta sanyawa motoci ba?in gilashi mai duhu wato “Tinted” ga kowane mai amfani da mota koshi waye.
IGP Alkali Baba Usman ya baiwa jami’an tsaron ?an sanda damar damke duk wanda suka sake kama motar sa dauke da ba?in gilashi mai duhu “Tinted” koshi waye.
IGP Alkali a ranar yau litinin 7 ga watan Yuni 2021, ya ce ya zama dole a haramtawa motoci sanya bakaken gilasai “Tinted” kasancewar bincike ya tabbatar ana amfani dashi wajen satar mutane a cikin birane da karkara a fa?in ?asar nan.
Ya ce, daga yanzu duk wanda suka sake samun motar shi da wannan bakin gilashin “Tinted” to zasu iya farfasa motar kuma su hukumta mai ita daidai da abunda doka ta tanada.
