Rahotanni daga Jihar Borno na bayyana cewar Kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta bayyana dalilinta na kashe shugaban kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, Abubakar Shekau, inda tace ya cancanci kisane shi yasa ta kashe shi.
A wani sakon cikin gida daga shugaban ISWAP, Abu Musab Albarnawi, wanda jaridar HumAngle ta samu a ranar Juma’a, ya ce Shekau ya kashe kansa ne bayan kin mika kai da yayi sakamakon kutsen da aka yi a maboyarsu a ranar 19 ga watan Mayun 2021.
Shugaban ISWAP yace shugaban rikon kwarya na ISIS na Iraq da Syria ya bada umarnin su dauka mataki kan Shekau saboda bijire musu da kuma kashe “masu imani” da yake yi. Kamar yadda yace, Shekau wanda ya karba ragamar Boko Haram bayan mutuwar Mohammed Yusuf a 2009, an kama shi a yanayi mai matukar tozarci.
“Wannan mutum ne da ya dinga ta’addanci. Mutane nawa ya salwantar? Mutane nawa ya halaka? Amma Allah ya bar shi tare da bashi tsawon rayuwa.
“A yayin da lokaci yayi, Allah ya ba sojojinmu nasara bayan sun karba umarni daga shugaban muminai,” Da farko ya gudu kuma ya fara yawo a dajikan Sambisa na kwanaki biyar inda ya sha matukar wahala.
Amma kuma mayakan ISWAP sun yi kokarin nemo shi. Har ila yau Abu Mus’ab ya bada labarin yadda Shekau ya sake tserewa a karo na biyu amma suka bi shi tare da kama shi.
Mayakan ta’addancin sun yi kira gareshi da magoya bayansa da su tuba, tare da tabbatar masa da cewa idan shugaban ISIS ya yanke hukuncin shugabantar da shi a kansu, basu da wani zabi da ya wuce biyayya garesa.
