Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Da Dama

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun hallaka manoma 12 tare da raunata wasu tara a kananan hukumomin Magami da Bayani a jihar Zamfara a yammacin jiya Juma’a.

Yan bindigan sun kuma sace dabbobi da wasu kayayyaki masu muhimmanci da a yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba.

An ruwaito cewa ‘yan bindigan sun kai harin ne a lokacin da manoman ke aiki a gonakinsu suna kokarin sharar gona domin shirin aikin daminan bana.

An kuma ruwaito cewa an birne mutanen 12 da aka kashe bisa koyarwa addinin musulunci yayin da wadanda suka samu raunuka suna asibiti suna karbar magani.

Related posts

Leave a Comment