Boko Haram, ISWAP Da IPOB Dangin Juna Ne – Soyinka

Fitaccen marubucin nan Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana kungiyar IPOB a matsayin ?anwa ga Boko Haram.

Soyinka ya bayyana haka ne duba da irin ?arnar da ‘yan IPOB ke yi musamman ma a yankin Kudu-maso-gabas inda su ke karkashe mutane da jami’an tsaro da lalata ofisoshin Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) da sauransu.

Da ya ke tsokaci kan batun haramta Tiwita a Najeriya, Farfesan ya ce gwagwarmayar tsagerun IPOB ba halastacciya ba ce.

Ya ce, “Ba na goyon bayan wa?anda suka ?uge da ?ona ofisoshin ‘yan sanda tare halaka jami’ansu, lalata ofisoshin za?e, yi wa ‘yan siyasa kisan gilla duk da zummar cimma manufofi na siyasa.”

Ya ci gaba da cewa wa?annan ma?arnata dangi ne na Boko Haram da ISWAP da sauransu, wa?anda bai kamata a yi kuskuren ?aukar su a matsayin masu neman halaliya ba.

A cewarsa a tarihin za?u??uka duk duniya, akan yi Allah wadai, ko ?aurace ma za?e da makamantan haka ba tare da ?aukar matakin kashe-kashen mutane da lalata dukiyoyin hukuma da na ?ai?aikun mutane ba.

Related posts

Leave a Comment