Bam ?in Soji Ya Hallaka Mahalarta Daurin Aure A Jihar Neja

Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar a wani harin bam da jirgin rundunar sojin sama ya gudanar a yankin garin Genu, jihar Neja, yayi sanadiyyar mutuwar wasu da suka halarci ?aurin aure, yayin da wasu da dama suka Jikkata.

Rahotanni sun bayyana cewa harin da jirgin ya?in ya kai ya kashe wasu makiyaya dake aikin satar shanu, kuma jirgin ya taso ne daga sansanin soji dake jihar Katsina.

Sai dai an gano cewa ?aya daga cikin bam ?in da jirgin ya jefa ya dira a wurin taron murnar ?aurin aure a Wani ?auyen jihar Neja, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya tabbatar.

Mutumin yace: “Mun hangi wani jirgi na sakin bam a ma?oyar yan bindiga, amma ?aya daga cikin bam ?in ya sauka a wurin taron murnar ?aura aure a ?auyen Argida.” “Biyu daga cikin mazauna ?auyen sun mutu, kuma mun gano cewa wasu ba?i da aka gayyato wajen taron sun ji raunuka.”

Amma da aka tuntu?i kakakin rundunar sojin sama, Edward Gabkwet, yace harin bam ?in da suka gudanar ya tafi yadda ake so cikin nasara. Yace: “Ba a kawo mana wani rahoton cewa harin ya shafi wa?anda ba ruwan su ba, manufar mu ita ce yan bindigan dake yankin Genu. Bayan mun samu rahoton fasaha cewa sun taru a yankin suna ?ulla shirin kaiwa mutane hari.”

Related posts

Leave a Comment