Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan Babagana Umara Zulum a ranar Alhamis ya jagoranci wani biki na ?addamar da mafarauta 1,000 da aka ?auka domin su shiga cikin sahun wa?anda ke ayyukan samar da tsaro a ya?in da ake yi da Boko Haram. Mafarautan za su fi mayar da hankalinsu ne wurin ba manoman da ke noma a wajen garin Jere kariya, wanda shi ne wurin da aka kashe manoma fiye da 70 a watan Nuwambar 2020. Wasunsu kuma za su yi aiki ne a…
Read MoreCategory: Tsaro
Tsaro
Zargin Cin Hanci: Shugaban ‘Yan Sanda Ya Bada Umarnin Bincikar Kyari
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sifeto Janar na hukumar yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya bada umurnin gudanar da bincike kan zargin da aka yiwa jami’in ‘yan sanda DCP Abba Kyari na karbar rashawa. Wannan na kunshe cikin jawabin da kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba, ya saki da yammacin Alhamis, 29 ga Yuli, 2021. A cewar Mba, hukumar na jaddadawa yan Najeriya cewa za’a bi gaskiya da adalci kuma za ta karfafa alakarta da takwararta ta Amurka, FBI. “Sakamakon zargi da tuhumar da hukumar…
Read MoreDa Dumi-Dumi: Kotu Ta Saki Zakzaky Da Matarshi
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta sallami Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu. A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke wa?anda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata. Wakilinmu a Kaduna ya ce jim ka?an bayan bayar da hukuncin ne aka fita da malamin a mota zuwa gida, inda ba su saurari ko ‘yan jarida ba. “Kotun ta sallame su ne saboda rashin ?wa??warar hujja,” a cewarsa.
Read MoreTabarbarewar Kasa: Ka Yi Gaggawar Sauka Daga Mulki – Gumi Ga Buhari
Shehin Malamin Musulunci, Gumi ya bukaci Shugaban kasa Buhari ya gaggauta murabus Laraba. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi tir da Gwamnatin Muhammadu Buhari Malamin ya ce gwamnatin tarayya ta gagara kare rayuka da dukiyoyin al’umma Shehin ya yi irin kiran da ya yi a baya, ya bukaci shugaban kasa ya yi murabus Kaduna – Malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Gumi, ya nemi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi murabus saboda matsalar tsaro. Gwamnatin Najeriya ba ta kare al’umma ba – Ahmad Gumi Sahara Reporters ta rahoto Sheikh Ahmad Abubakar…
Read MoreAn Tura Mataimakan Shugaban ‘Yan Sanda 24 Shiyyoyin Kasa
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Usman Alkali Baba, Sufeto-Janar na ’Yan sanda ya ba da umarnin aikawa tare da sauyawa mataimakan Sufeto-Janar na ‘Yan sanda 24 (AIGs) mukamai da kuma wuraren aiki na shiyyoyi. A cewar wata sanarwa data fito a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda, CP Frank Mba, sauya wuraren aikin ya dace da sabuwar manufar ci gaban ‘Yan Sandan Najeriya. Sanarwar ta nuna cewa AIG Bala Ciroma zai koma shiyya ta 7 Abuja yayin da AIG Usman Belel,…
Read MoreDa Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Tilasta El Rufa’i Dakatar Da Bude Makarantu
Gwamnatin Kaduna ta dakatar da bu?e makarantu a fa?in jihar har sai baba ta gani. Gwamna Nasir El-Rufai ne ya sanar da hakan ne a taron masu ruwa da tsaki a wannan Litinin ?in. El Rufai ya ce gwamnati ta yanke wannan shawarar ne saboda matsalolin tsaro da ke addabar sassan jihar. Ya kuma shaida cewa gwamnati na iya ?o?arinta wajen kare yara da ?alibai daga hare-haren ?an bindiga. Gwamnan ya ce an tura ?arin jami’an tsaro jihar domin ya?ar ?an bindiga don haka yana mai gargadin mazauna Kaduna su…
Read MoreKaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Masarautar Jaba
Rahotannin da muke samun a halin yanzu daga Jihar Kaduna na cewa yan bindiga sun sace wani Sarki mai daraja ta daya Sarkin Masarautar Jaba Kpop Ham, Dokta Jonathan Danladi Gyet Maude (JP, OON) wanda sanannen Sarki ne kuma jagoran al’ummar Jaba cikin Jihar Kaduna. Rahotannin da muke samu na bayanin cewa an sace shi ne a Gonarsa da ke Jihar Nasarawa. Rundunar tsaro ta Yan Sanda a Jihar Kaduna na cewa su na nan su na tuntubar abokan aikinsu daga Jihar Nasarawa, domin sanin ko yaushe lamarin ya faru.…
Read MoreSokoto: ‘Yan Bindiga Sun Nausa Da Fasinjoji Sama Da 50 Dokar Daji
Akalla matafiya 50 ‘yan bindiga suka sace a Sokoto, kamar yadda wani shaidar gani da ido ya bayyana. Jaridar PREMIUM TIMES ta ambatocewa wani babban jami’in gwamnati ne ya tabbatar mata da hakan, sai dai bai bayyana mata adadin mutanen da aka sace ba. Matafiyan suna tafiya ne daga Sokoto zuwa Gusau lokacin da aka sace su a ranar Lahadi. Ba dai a tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba a safiyar ranar Lahadin, amma wadanda suka ga faruwar lamarin sun ce mutanen da aka sace sun kai 50. Majiyoyi…
Read MoreKaduna: An Ceto Dalibai 28 Cikin Wadanda Aka Sace A Kwalejin Bethel Baptist
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Jami’an ‘yan sandan Nijeriya sun yi nasarar sake kubutar da yara ashirin da takwas daga cikin yaran da aka sace a makarantar Bethel Baptist High Secondary School ta Jihar Kaduna. An yi nasarar kubutar da su ne yau Lahadi, inda tuni iyayensu suka karbe su a harabar makarantar. A watan da ya gabata ne wasu gungun ‘yan Bindiga suka dira Makarantar ta Bethel Baptist, inda suka yi awon gaba da dalibai kimanin 200 cikin dokar daji. Jihar Kaduna dai na fuskantar barazanar ‘yan…
Read MoreDa ?umi-?umi: An Yi Yunkurin Hallaka Sarkin Kano
Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero, ya tsallake wani yunkuri na kai masa hari da wani da ba a san ko waye ba ya yi kokarin buge motarsa. A cewar wani ganau da ya zanta da majiyarmu ya ce lamarin ya faru ne lokacin da Sarkin ke shirin komawa fadarsa kusa da titin Zariya, a cikin Kano. Tuni dai ‘yan sanda suka cafke wanda ake zargin. Sai dai, ba a bayyana dalilin kai harin ba. Har yanzu ‘yan sanda ba su ba da sanarwar abin da suka gano ba.
Read MoreNeja: ‘Yan Bindiga Sun Ki Sakin Daliban Islamiyya Bayan Karbar Miliyan 55
Iyayen daliban Islamiyyar Salihu Tanko su 156 da akayi garkuwa dasu a Tegina, dake karamar hukumar Rafi a jihar Niger sun koka kan cewa barayin yaran sun ki sako daliban duk da an basu kudin fansa har Naira Miliyan 55. Shugaban makarantar Malam Alhassan Garba Abubakar, ya shaidawa majiyarmu cewa da farko sun tura Naira miliyan 25 amma bayan kwanaki 3 sai masu garkuwar suka ce anyi kuskure ba su aka baiwa kudin ba, wasu gungun aka baiwa saboda haka sai a sake turo masu Milyan 30. Alhassan ya ce…
Read MoreKaduna: ‘Yan Fashi Sun Yi Gaba Da Takardun Jarrabawa Bisa Zaton Kudi Ne
Wasu ‘yan fashi da makami a safiyar ranar Juma’a sun kai hari kan makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Unguwar Sarki, a cikin tsakiyar garin Kaduna inda suka tafi da takardun jarrabawa da aka shirya wa daliban aji shida wadanda za su rubuta jarrabawar karshe ta NECO bisa tsammanin cewa kudade ne.‘Yan bindigar da suka kutsa kai cikin makarantar sun nemi jami’ar da ke kula da NECOn da ta mika musu takardun jarrabawar duk da cewa ta yi kokarin bayyana musu takardun jarrabawar ne ba kudade ba. An gano cewa sun…
Read MoreAmurka Ta Rufe Asusun Ajiyar Kungiyar Tsagerun Inyamurai
Rahotanni daga ?asar Amurka na bayyana cewar wani Banki dake kasar ya rufe asusun ajiyar ?ungiyar Tsagerun Inyamurai ta IPOB ?arkashin jagorancin Nnamdi Kanu dake garkame a Najeriya. A cewar rahoton Sanarwar da Chika Edoziem, shugaba a kungiyar ta IPOB, ya fitar a ranar Alhamis ta ce ana amfani da asusun ajiyar ne domin karbar kudaden da mambobin IPOB ke biya duk wata. Edoziem ya ce an rufe asusun ajiyar ne biyo bayan samun rahoto daga bankin na cewa wasu mutane da ba a bayyana ko su wanene ba suka…
Read MoreKano: An Kama Matasan Da Suka Yi Luwadi Da Wani Saurayi
An kama Mutane biyar a Kano da suka yiwa wani Dan Shekara 20 fyade a Jahar Kano Wannan na kunshe ne a cikin sanarwa da Mai Magana da Yawun Rundunar Yansandan Jahar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a Kano. Yansandan sunce wata mata dake zama a unguwar Mandawari dake Kano, ta kawo rahoton a ofishin Yansanda. Yansanda sunce wadanda aka kama sun hada da Ahmed Inuwa Dan Shekaru 34, da Nasiru Isyaku Dan Shekaru 48, da Lawan Uba Dan Shekaru 31 da Kuma Auwal Uba Dan Shekaru 40 gami…
Read MoreAdamawa: An Cafke Wanda Ya Kashe Matarshi Ta Hanyar Dukan Tsiya
A yanzu haka rundunan yan sandan jahar Adamawa na tsare da wani magidanci mai dan shekaru arba in da daya mai suna Usman Hammawa bisa zarginsa da yiwa matarsa mai suna Rabiyatu Usaman yar shekar talatin da shida duka wanda hakan yayi sanadiyar tafiyarta lahira. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yola. D S P Suleiman yace an kama mutumin ne a anguwar Jada dake cikin karamar hukmar Ganye a jahar…
Read MoreTakarar Shugabancin Kasa Ya Kamata Ku Fito Ba Hatsaniya A Kasa Ba – Kungiya Ga Kanu Da Igboho
Wata kungiya mai suna ‘Africa’s New Dawn’ ta bukaci ?an gwagwarmayar Yarbawa, Sunday Igboho da Nnamdi Kani, shugaba IPOB su yi watsi da gwagwarmayarsu su fito takarar shugaban kasa a 2023 maimakon kokarin tayar da fitina a ?asa. Shugaban kungiyar na kasa, Iluckukwu Chima, yayin da ya ke sanar da taron wayar da kan mutane da za su yi mai taken, ‘One Love, One Nation, One President’, a ranar Alhamis a Abuja ya ce zaman Nijeriya a matsayin ?asa guda ya fi alheri ga kowa. Yayin da gwamnatin Nijeriya ke…
Read MoreJiragen Yakin Da Najeriya Ta Sayo Daga Amurka Sun Iso Najeriya
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar sojojin saman Nigeria, NAF, a ranar Alhamis ta karbi rukuni na farko na jiragen sama na yaki kirar A-29 Super Tucano daga kasar Amurka. Edward Gabkwet, direktan sashin hulda da jama’a da watsa labarai na hedkwatar rundunar sojojin saman Nigeria da ke Abuja ne ya sanar da hakan ga manema labarai. Kakakin sojojin saman ya ce jiragen sun iso jihar Kano ne misalin karfe 12.34 na rana. Bashir Magashi, Ministan tsaro; Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin kasa; da Oladayo Amao, babban…
Read MoreLauyan Igboho Ya Fallasa Halin Kunci Da Yake Ciki
Babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin inda ake azabtar dashi tamkar dabba. Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da manema labarai a daren ranar Talata. Ya ce ?an sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ?akin ajiye wadanda ake zargi da laifi. Ya ce: “Sun ?aure shi…
Read MoreTaraba: Masarautar Muri Ta Ba Makiyaya Wa’adin Wata Guda Su Bar Yankin
Rahotanni daga Jihar Taraba na bayyana cewar Sarkin masarautar Muri a jihar, Abbas Tafida ya ba da wa’adin kwanaki 30 ga makiyaya da ke addabar mazauna yankin kan su bar dazuzzukan fadin masarautar ko kuma a tilasta musu yin hakan. Rahotanni sun bayyana cewa Sarkin ya bayar da wa’adin ne a ranar Talata bayan sallar Idi. Wannan ya biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane, kashe-kashe, da hare-hare a jihar da wasu miyagu da ake zargin makiyaya ne ke aikatawa. Basaraken Ya yi ikirarin cewa Fulani makiyaya ne ke da alhakin aikata…
Read MoreZa Mu Zakulo Gami Da Hukunta Masu Haddasa Fitina A Najeriya – Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa za a ci gaba da kokarin zakulo masu son haddasa fitinan kasar dake addabar mutane, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Shugaban kasar ya fadi hakan ne bayan kammala Sallar Idin Layya a gidansa da ke Daura a jihar Katsina, a ranar Talata. Duk da cewa bai bayar da misali ko ambatar sunan wani ba, amma kalaman nasa na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da aka kama mai fafutukar kafa kasar Yarabawan nan Sunday Adeyemo, da aka fi sani da Sunday…
Read More