Adamawa: An Cafke Wanda Ya Kashe Matarshi Ta Hanyar Dukan Tsiya

A yanzu haka rundunan yan sandan jahar Adamawa na tsare da wani magidanci mai dan shekaru arba in da daya mai suna Usman Hammawa bisa zarginsa da yiwa matarsa mai suna Rabiyatu Usaman yar shekar talatin da shida duka wanda hakan yayi sanadiyar tafiyarta lahira.

Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yola.

D S P Suleiman yace an kama mutumin ne a anguwar Jada dake cikin karamar hukmar Ganye a jahar Adamawa, biyo bayan rahoton da yan uwara marigayiyar suka kai a ofishin yan sandan dake karamar hukumar ta Ganye.

Lamarin ya farune dai sakamokon ta kaddama da yaru a tsakaninsu a lokacin da matar ta nemi da ya biyata kudinta da ya ranta wanda kuma hakan ya fusata mai gidan tare da buga kanta a jikin gini wanda haka yasa tafadi sume inda aka gaggauta da ita zuwa asibiti kafin nan ma da mutu.

Sanarwa ya cigaba da cewa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa C P Aliyu Adamu ya yabawa rundunan dama yan Sakai da ke taimakawa yan sandan bisa na mijin kokari da sukeyi na kama masu aikata laifuka a tsakanin al umma.

Harwayau sanarwa ya baiyana cewa kafin rasuwa Rabiyatu dai sun kwashe shekaru sha shida harma suna da yara biyar a tsakanin su.

Related posts

Leave a Comment