Borno: An Horas Da Mafarauta 1000 Domin Fuskantar Boko Haram

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan Babagana Umara Zulum a ranar Alhamis ya jagoranci wani biki na ?addamar da mafarauta 1,000 da aka ?auka domin su shiga cikin sahun wa?anda ke ayyukan samar da tsaro a ya?in da ake yi da Boko Haram.

Mafarautan za su fi mayar da hankalinsu ne wurin ba manoman da ke noma a wajen garin Jere kariya, wanda shi ne wurin da aka kashe manoma fiye da 70 a watan Nuwambar 2020.

Wasunsu kuma za su yi aiki ne a wasu yankunan birnin Maiduguri da kuma ?ananan hukumomin Konduga da Mafa.

An ?addamar da mafarauta 1,000 ne a gundumar Gongulong, bayan dukkansu sun tsallake binciken da hukumomin tsaro na DSS da na sojojin Najeriya su ka yi mu su.

Gwamnan jihar ta Borno na ?okarin samar da mafita ga matsalar rashin tsaro a yankin ta hanyar ?aukar dubban ?an sa-kai da mafarauta tare da taimakon sojojin Najeriya.

Baya ga wannan, akwai kuma shirin samar da ilimi da bayar da tallafi ga gajiyayyu da wa?anda rikicin na Boko Haram ya ?ai?aita.

Related posts

Leave a Comment