Takarar Shugabancin Kasa Ya Kamata Ku Fito Ba Hatsaniya A Kasa Ba – Kungiya Ga Kanu Da Igboho

Wata kungiya mai suna ‘Africa’s New Dawn’ ta bukaci ?an gwagwarmayar Yarbawa, Sunday Igboho da Nnamdi Kani, shugaba IPOB su yi watsi da gwagwarmayarsu su fito takarar shugaban kasa a 2023 maimakon kokarin tayar da fitina a ?asa.

Shugaban kungiyar na kasa, Iluckukwu Chima, yayin da ya ke sanar da taron wayar da kan mutane da za su yi mai taken, ‘One Love, One Nation, One President’, a ranar Alhamis a Abuja ya ce zaman Nijeriya a matsayin ?asa guda ya fi alheri ga kowa.

Yayin da gwamnatin Nijeriya ke tsare da Kanu, Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho yana hannun jami’an tsaro a Jamhuriyar Benin bayan kama shi a filin tashin jirage na Bernardin tare da matarsa a hanyarsu na zuwa Jamus a daren ranar Litinin.

An ruwaito cewa Chima ya ce Nigeria kasace da ake kwatance da ita a nahiyar Afirka, yana mai cewa tarwatsa kasar zai janyo wa nahiyar matsala a duniya.

“Nijeriya ce ?asar Afirka da duniya ta sani. Idan muka lalata Nijeriya saboda ?alubalen da muke fuskanta, wace kasar muke da shi? Rabuwa ba shine mafita ba. Maganin abin shine ?aunar juna.

“Sai dai wasu suna son kafa gwamnatinsu. Igboho da Kanu na son kafa ?asa a cikin wata ?asa. Hakan ba zai iya faruwa ba domin Nigeria ta fi kowane mutum ?aya. “Duk wanda ke son kafa gwamnati ya yi ha?uri, ya gina jam’iyyar siyasa ya yi takara a 2023.

A lokacin, masu zabe za su zabi abin da suke so. Kundin tsarin mulki ya ce a ri?a zabe bayan shekaru hudu kuma zaben zai fitar mana da shugaban ?asa.”

Related posts

Leave a Comment