Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sifeto Janar na hukumar yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya bada umurnin gudanar da bincike kan zargin da aka yiwa jami’in ‘yan sanda DCP Abba Kyari na karbar rashawa.
Wannan na kunshe cikin jawabin da kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba, ya saki da yammacin Alhamis, 29 ga Yuli, 2021.
A cewar Mba, hukumar na jaddadawa yan Najeriya cewa za’a bi gaskiya da adalci kuma za ta karfafa alakarta da takwararta ta Amurka, FBI.
“Sakamakon zargi da tuhumar da hukumar FBI ta yiwa daya daga cikin jami’an yan sandan Najeriya, DCP Abba Kyari, Sifeto Janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba ya bada umurnin duba abun.” “Duk yadda ta kaya za’a sanar da jama’a.”
